Abun mamaki: Bidiyo da hotunan yadda Firayim ministan Ethiopia ya koma 'direban' Buhari

Abun mamaki: Bidiyo da hotunan yadda Firayim ministan Ethiopia ya koma 'direban' Buhari

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai taba tsammanin akwai karamcin da zai riska ba bayan isar sa kasar Ethiopia a ranar 3 ga watan Oktoba
  • Firayim ministan kasar kuma babban jami'i a gwamnatin ya karba shugaban kasa Buhari a filin saukar jiragen da ke Addis Ababa bayan isarsa
  • Hakazalika, da kan shi firayim ministan ya dauka mota inda ya tuka shugaban kasa Buhari zuwa wani lambu domin cin abincin dare

Addis Ababa,Ethiopia - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu karba mai kyau tare da karamci bayan isar sa kasar Ethiopia domin rantsar da sabon firayim ministan kasar, Abiy Ahmed.

Bayan isar shugaban kasa Muhammadu Buhari Addis Ababa, babban birnin kasar, ya samu tarba mai kyau daga Ahmed, shugaban kasan, Sahle-Work Zewde da shugaban Senegal, Marcky Sall Zewde.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya maida wa Sanusi martani kan ikirarin cewa tattalin Najeriya ya kusa ya ruguje

Abun mamaki: Bidiyo da hotunan yadda Firayim ministan Ethiopia ya koma 'direban' Buhari
Abun mamaki: Bidiyo da hotunan yadda Firayim ministan Ethiopia ya koma 'direban' Buhari. Hoto daga Buhari Sallau
Asali: Facebook

Dakarun tsaron kasar Ethiopia sun ba shi cikakken girmamawa bayan isar sa kasar, PM News suka ruwaito.

Duk wannan bai isa ba, Ahmed, firayim ministan kasar ya dauka mota da kan shi inda ya tuka shugaban kasa Buhari zuwa wani sabon lambu da aka gina domin cin abincin darensu.

Hotuna da bidiyon wannan al'amari mai dadi sun fito ne daga shafin hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Buhari Sallau, a Facebook.

Rekeb, gagararren dan bindiga ya sanar da dalilinsu na yunkurin kafa sansani a Sabon Birni

A wani labari na daban, wasu 'yan bindiga da ke jihar Zamfara an gano cewa suna garzayawa yankin Sabon Birni da ke jihar Sokoto domin suna tsammanin zuwan dakarun sojin Nijar da ke kokarin taimakon Najeriya wurin shawo kan matsalar 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2022 a ranar Alhamis ga majalisar dokoki

Wani shugaban 'yan bindiga ya ce suna kokarin kafar sansani a kauyukan Ballazu da Gangara na yankin, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Sabon Birni karamar hukuma ce da ke tsakanin iyakokin Nijar da wasu kauyuka da ke kan iyaka. An dinga samun farmakin miyagu a Sabon Birni da kananan hukumomi masu makwabtaka a cikin kwanakin nan inda har suka hada da sansanin soji da ke Burkusuma ina a kalla jami'ai 15 suka rasa rayukansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng