Da duminsa: FG ta bada hutun ranar Juma'a, 1 ga watan Oktoba

Da duminsa: FG ta bada hutun ranar Juma'a, 1 ga watan Oktoba

  • Gwamnatin tarayya ta fitar da ranar Juma'a, 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu a Najeriya
  • Ministan tsaron cikin gida, Rauf Aregbesola, ya ce an bada hutun ne domin murnar cikar kasar shekaru 61 da samun 'yancin kai
  • Aregbesola ya ce wannan cigaba ne da ya zama dole a yi shagalinsa amma hankalin shugaban kasa na kan kiyaye yaduwar cutar korona

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma'a, 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu domin cikar Najeriya shekaru 61 da samun 'yancin kai, Daily Nigerian ta ruwaito.

Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola wanda ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya kamar yadda ya ke dauke a takardar da babban sakataren ma'aikatar, Dr Shuaib Belgore ya sa hannu.

Da duminsa: FG ta bada hutun ranar Juma'a, 1 ga watan Oktoba
Da duminsa: FG ta bada hutun ranar Juma'a, 1 ga watan Oktoba. Hoto daga dailynigerian.com
Source: UGC

Kamar yadda takardar tace, ministan na taya dukkan 'yan Najeriya murnar cikar kasar nan shekaru 61 kuma ya tabbatar da cewa gwamnati ta mayar da hankali wurin kawo karshen dukkan kalubale, kama daga na siyasa, tattalin arziki da sauransu.

Read also

El-Rufai zai rusa dubunnan gidaje a Garin Zaria, Gwamnati za ta tada Unguwa sukutum

"Kasa mai dauke da mutum miliyan 200 da doriya mai cike da hazikan mutane, ma'adanai da sauransu. 'Yan Najeriya na walwali tamkar lu'u-lu'u a wuraren da suka hada da makarantu, kasuwanci, kirkira, waka, fina-finai, nishadi, al'adu da sauransu.
"Babu shakka mu ne kasar bakar fata da ke jagoranci a duniya kuma babu shakka mu ne abun alfahari da dogaron Afrika," Aregbesola yace.

Ministan ya tabbatar da cewa, shagalin cikar Najeriya shekaru 61 ya zama dole, amma kuma kariyar 'yan Najeriya shi ne babban abinda shugaban kasa ya saka gaba, ballantana kan yadda cutar korona mai nau'in Delta ta ke nan. Don haka za a yi shagalin wannan shekarar ba kamar yadda aka saba ba.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a yayin yi wa 'yan Najeriya fatan shagali mai dadi, ya tunatar da su cewa iyayenmu duk da banbancinsu a addini, kabila da yare, sun hadu tare da yin shagalin bikin samun 'yancin kai tare.

Read also

Jami'an NSCDC sun cafke abokin harkallar 'yan bindiga dauke da karamar bindiga

A don haka ya yi kira ga 'yan Najeriya da su tattaro tare da hada kai da wannan mulkin wurin tabbatar da cewa Najeriya ta dukkan 'yan kasa ce, gida da waje a cigaba da yadda jajirtattun da suka samar mana da 'yanci suka yi.

Farmaki: Mazauna wasu garuruwa a Kaduna sun bar gidajensu, suna neman daukin gwamnati

A wani labari na daban, a ranar Talata, jami'an tsaro sun kara samo gawawwaki uku a kauyukan Madamai da Kacecere da ke kananan hukumomin Kaura da Zangon Kataf, lamarin da yasa yawan mamatan ya kai har arba'in da biyar.

Daily Trust ta tattaro cewa, za a yi birniyar wasu daga cikin mamatan a kauyen Madamai da ke karamar hukumar Kaura a ranar Alhamis yayin da aka birne wasu kamar yadda addinin Islama ya tanada a ranar Litinin a karamar hukumar Zangon Kataf.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan a ranar Talata ya ce rahotannin tsaro sun bayyana cewa an sake samun karin gawawwaki 3, biyu daga harin Madamai, daya kuma a harin Kacecere.

Read also

An cafke wani sojan karya da abokinsa da ke samar wa da 'yan bindiga hanyoyin sadarwa

Source: Legit.ng

Online view pixel