El-Rufai zai rusa dubunnan gidaje a Garin Zaria, Gwamnati za ta tada Unguwa sukutum

El-Rufai zai rusa dubunnan gidaje a Garin Zaria, Gwamnati za ta tada Unguwa sukutum

  • Gwamnatin Nasir El-Rufai tana shirin rusa gidajen da ke Graceland a Garin Zaria
  • Ana tunani wannan rushe-rushe da za ayi zai shafi gidaje 10000 da mutum 200000
  • Ba wannan ne karon farko da gwamnatin jihar Kaduna ta rusa gidajen al’umma ba

Kaduna - Rahotanni daga jaridar Leadership sun bayyana cewa Gwamnatin Mai girma Nasir Ahmed El-Rufai za ta rusa gidaje da dama a garin Zariya.

Kamar yadda muka samu labari, gwamnati za ta rusa gidaje da gine-ginen al'umma a unguwar da ake kira Graceland da ke karamar hukumar Sabon Gari.

Wannan unguwa tayi makwabtaka da makarantar koyon tukin jirgin sama da ke hanyar Samaru, ana zargin filayen unguwar sun shiga cikin filin makarantar.

Jaridar Leadership tace gwamna Nasir El-Rufai yana zargin dubunnan mutanen da ke wannan yanki da mallakar filaye ba tare da sun bi ka’idojin mallaka ba.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kame waɗanda ake zargi da kisan babban malamin Addini a jihar Kano

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa mutane suna ta kuka a kan wannan mataki da gwamnati ta dauka, inda aka baza jami’an tsaro da nufin a rusa unguwar.

El-Rufai
Gwamnan Kaduna, Malam El-Rufai Hoto: @elrufai
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Muna da takardun mallaka - Mai unguwa

Wani mai unguwa a yankin Graceland, Gunji Makama ya shaida wa manema labarai cewa abin da gwamnan Kaduna yake kokarin yi, ya ci karo da dokar kasa.

Gunji Makama yace mazauna unguwar sun mallaki takardu kafin su gina gidajen da suke ciki.

Mutanen garin Zaria sun tabbatar mana da cewa an baza manyan motoci da ke tunbuke gine-gine a unguwar Graceland, ana jiran a fara ruguza gidajen jama’a.

Wata majiya ta shaida mana cewa babu abin da zai hana gwamnatin jihar rusa gidajen sai ikon Allah. Motocin jami’an tsaro sun cika gari domin hana rikici.

Leadership tace ana tunani mutane 200, 000 za su rasa matsuguni idan aka rusa wadannan gidaje da adadinsa ya kai 10, 000 a wannan unguwa da ke garin Zaria.

Kara karanta wannan

NAFDAC ta gargadi 'yan Najeriya da su daina cin daskararrun kaji da talo-talo

Gwamna Rusau?

Kwanakin baya aka ji Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai yana cewa wanda zai gaje shi a mulki a shekarar 2023 sai ya yi rushe-rushe sama da yadda ya yi.

Gwamna El-Rufai ya koka game da yadda jama'a suke zaginsa, suka kosa ya sauka daga kan mulki duk da cewa gwamnatinsa ta taimaka wa mutanen Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel