Farmaki: Mazauna wasu garuruwa a Kaduna sun bar gidajensu, suna neman daukin gwamnati

Farmaki: Mazauna wasu garuruwa a Kaduna sun bar gidajensu, suna neman daukin gwamnati

  • Jami'an tsaro a kananan hukumomin Kaura da Zangon Kataf na jihar Kaduna sun sake gano gawawwaki 3 a yankunan
  • Tuni mazauna kauyukan Madamai da Kacecere suka fara tattara komatsansu inda suke gudun hijira zuwa birane
  • Sun koka da halin da suka tsinci kansu inda suke kira ga gwamnati da ta kawo musu dauki da gaggawa

Kaduna - A ranar Talata, jami'an tsaro sun kara samo gawawwaki uku a kauyukan Madamai da Kacecere da ke kananan hukumomin Kaura da Zangon Kataf, lamarin da yasa yawan mamatan ya kai har arba'in da biyar.

Daily Trust ta tattaro cewa, za a yi birniyar wasu daga cikin mamatan a kauyen Madamai da ke karamar hukumar Kaura a ranar Alhamis yayin da aka birne wasu kamar yadda addinin Islama ya tanada a ranar Litinin a karamar hukumar Zangon Kataf.

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

Farmaki: Mazauna wasu garuruwa a Kaduna sun bar gidajensu, suna neman daukin gwamnati
Farmaki: Mazauna wasu garuruwa a Kaduna sun bar gidajensu, suna neman daukin gwamnati. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan a ranar Talata ya ce rahotannin tsaro sun bayyana cewa an sake samun karin gawawwaki 3, biyu daga harin Madamai, daya kuma a harin Kacecere.

Kamar yadda Aruwan ya ce, ana cigaba da ayyukan nema tare da ceto wasu. Amma kuma Daily Trust ta gano cewa, wadanda suka sha da kyar daga harin Kacecere sun tsere zuwa Zangon Kataf domin neman mafaka.

Shuaibu Tanimu, daya daga cikin wadanda suka tsallake harin da baya sun sanar da Daily Trust cewa sun bar gidajensu domin tserar da rayukansu duk da mutum hudu sun bace.

Wani mazaunin kauyen Madamai da ke karamar hukumar Kaura, Derek Christopher, ya ce da yawa daga cikin mazauna yankin sun rasa gidajensu sakamakon hare-haren. Sun koma yankunan kusa saboda babu sansanin 'yan gudun hiijira.

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

A yayin bada labarin abinda ta fuskanta, tsohuwa mai shekaru 79 a Zangon Kataf wacce ta bada sunanta a Habiba Ibrahim, ta ce miyagun sun tsinke mata hannunta da adda inda suka bar ta cikin jini.

Ta sanar da cewa an fara kai ta asibitin tunawa da Sir Patrick Ibrahim Yakowa da ke Kafanchan, kafin daga bisani a mika ta wani asibiti da ba a bayyana ba tare da wasu mutum hudu domin samun taimakon likitoci.

Osinbajo ya bayyana halin da yankunan kasar nan za su shiga idan Najeriya ta rabu

A wani labari na daban, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce 'yan Najeriya ne za su wahala idan aka raba kasar nan.

Ya sanar da hakan ne a ranar Litinin yayin da ya karba bakuncin shugabannin kungiyar 'yan jarida na kasa a fadar Aso Villa da ke Abuja.

Kamar yadda takardar da Laolu Akande, mai magana da yawun Osinbajo ya fitar, ya ce akwai bukatar a karfafa hadin kai a kasar nan kuma ya shawarci 'yan jarida da su kasance masu kwarewa yayin sauke nauyin da ke kansu.

Read also

Ganawar gwamnonin Arewa: Abubuwa 5 masu muhimmanci da suka cimma a taron

Source: Legit

Online view pixel