Jami'an NSCDC sun cafke abokin harkallar 'yan bindiga dauke da karamar bindiga
- Jami'an tsaron NSCDC sun cafke wani matashi da ake zargin yana hada kai da 'yan bindiga
- An kama shi da makami da kuma wayoyi guda biyu, inda ya amsa cewa yana hade da wasu 'yan bindiga
- A cewarsa, ya mallaki bindigar ne saboda ya kare kansa ya kuma dauki fansar barayin da suka masa fashi
Enugu - Hukumar tsaro ta NSCDC, ta cafke wani da ake zargi mai hada gwiwa ne da kuma ba 'yan bindiga bayanai wajen garkuwa da mutane da ke barna a cikin garin Enugu da kewayenta, Daily Nigerian ta ruwaito.
Hukumar ta kwato N2,100, katunan ATM guda uku, wayoyin hannu guda biyu, kunshin wani abu da ake zargi tabar wiwi ne da kuma karamar bindiga da aka boye a karkashin wasu abubuwan a cikin karamar jaka da sauransu.
Jami'in hulda da jama'a na hukumar NSCDC, reshen jihar Enugu, Danny Manuel, ya fada a cikin wata sanarwa ranar Lahadi a Enugu cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar 30 ga Satumba.
Mista Manuel, ya ce jami'ansu sun kama shi ne yayin aikin sintiri a yankin WTC Estate na Enugu da misalin karfe 2 na rana bayan daliban da suka dawo daga makaranta sun hango shi yana rike da bindiga wajen yin fashi ga wani mutum a yankin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa, wanda ake zargin shine Oguchi Oguamanam, namiji mai shekaru 24, wanda ke zaune a 7 Monarch Avenue daura da Timber Junction kusa da garin Ugwu-Aji a cikin garin Enugu.
Kakakin NSCDC ya ce:
“Lokacin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya yarda cewa yana aiki ne da wani gungun 'yan ta'adda da ke zaune a Legas.
"Ya bayyana cewa gungun nasu galibi suna tura masa kudi a cikin asusun sa wanda zai cire su kuma ya saka a cikin kowane asusun da suka aiko masa sannan a ciki yana daukar nasa rabon..
“Ya kuma yi ikirarin cewa wasu gungun samari sun taba yi masa fashi a cikin gida kuma ya shirya bindiga don amfani da ita azaman dabarar daukar fansa a duk lokacin da ya ga wani daga cikin yaran.
"Ya ce daya daga cikin wayar salula da aka samu a hannunsa mallakar sa ce, amma game da wayar android ba zai iya bayanin yadda ya same ta ba."
Mista Manuel ya ba mazauna yankin tabbacin cewa za su hada kai da hukumomin tsaro a jihar don karewa da kuma tsare mutane a kowane lokaci.
An cafke kasurgumin kwamandan 'yan bindigan da ya addabi jihar Zamfara
Ayuba Elkanah, kwamishinan 'yan sanda a Zamfara, ya ce rundunar 'yan sanda ta cafke wani kasurgumin kwamandan 'yan bindiga mai suna Bello Rugga, The Cable ta ruwaito.
Elkanah ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da yake gabatar da wanda ake zargi kwamanda ne tare da wasu mutane 21 da ake zargi da fashi da makami a Gusau.
Ya ce an kashe wasu 'yan bindiga biyar yayin wani samame da suka kai a karamar hukumar Gummi ta jihar.
A cewarsa:
"A ranar 1 ga Oktoba, 2021, 'yan sanda masu dabarun yaki da 'yan ta'adda a kewayen Gummi, sun yi aiki da rahoton bayanan sirri, sun kai hari Gidan Bita, Malanjara da dajin Kagara, suka kama wani kasurgumin kwamandan 'yan bindiga, Bello Rugga."
“Wanda ake zargin ya kasance kwamanda ga wani shugaban yan ta’addan da ake nema, wanda aka fi sani da Turji.
“Rugga shine ke kula da Gummi, Gidan Bita, Malanjara da Kagara da ke karamar hukumar Gummi ta jihar.
"Ya shirya jerin hare-hare a yankin wanda ya kai ga kisan gilla ga mutanen da ba su ji ba ba su gani ba tare da yin garkuwa da wasu da yawa don neman kudin fansa.
Rahoto: Halin da ake ciki na harin 'yan bindiga duk da katse hanyoyin sadarwa a Zamfara
A wani labarin, alamu sun bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da samun kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihar Zamfara duk da katse hanyoyin sadarwa a jihar.
Yayin da katsewar da kokarin sojoji ya rage barnar 'yan bindiga tare da kashe su, wasu mazauna jihar sun shaida wa BBC Hausa cewa an ci gaba da kai hare-hare da sace-sacen a jihar.
Don haka, duk da rokon da suke yi wa gwamnatin jihar na tsagaita wuta, kamar yadda Gwamna Bello Matawalle ya bayyana a ranar 10 ga Satumba, 'yan bindigan sun ci gaba da kai hari kan mazauna jihar.
Asali: Legit.ng