Sojin sama sun sheke mutum 28 da ke kai wa 'yan ISWAP kayan bukata a Kukawa

Sojin sama sun sheke mutum 28 da ke kai wa 'yan ISWAP kayan bukata a Kukawa

  • Dakarun sojin Najeriya sun sheke rayuka 28 na wasu da ke kai wa 'yan ta'addan ISWAP kayayyakin bukata
  • Majiyar tsaro ta ce wadanda aka yi wa luguden wuta masu kai wa 'yan ta'addan makamai, man fetur da kasuwancin kifi
  • Har ila yau, masuntan da aka sheke duk masu hada kai da 'yan ta'addan ne kuma an haramta kamun kifi a kogin

Kukawa, Borno - A kalla 'yan ta'adda 28 da ke da alaka da Islamic State of the West African Province (ISWAP) tare da masu basu hadin kai a kasuwancin kifi ne suka hadu da ajalinsu a ranar Lahadi, PRNigeria ta tattaro hakan daga majiyoyin sirri.

Majiyoyin da aka tura yankin arewa maso gabas a jihar Borno, sun ce mayakan da masu basu hadin kai da suka hada da masunta an kashe su ne sakamakon shiryayyen harin dakarun kasa da na sama wanda sojin suka hada a Daban Masara da ke karamar hukumar Kukawa ta jihar.

Kara karanta wannan

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa kan ta tuba, aure ya mutu

Sojin sama sun sheke mutum 28 da ke kai wa 'yan ISWAP kayan bukata a Kukawa
Sojin sama sun sheke mutum 28 da ke kai wa 'yan ISWAP kayan bukata a Kukawa. Hoto daga PRNigeria.com
Asali: UGC

PRNigeria ta tattaro cewa, bayan bayanan sirrin da aka samu har aka kai farmakin, an yi nasarar sheke miyagu ashirin da ke taimaka wa 'yan ta'addan da kayayyakin bukata.

Daban Masara na nan a arewacin tsakar dajin Chadi, kusan tafiyar sa'o'i biyu daga garin Kukawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda majiyar rundunar sojin ta ce, wurin an saba ganin 'yan ta'adda wanda kuma ya zama wurin haduwarsu domin karbar makamai, man fetur, kayan abinci, babura da sauran ababen bukata da ake kai musu.

"A wurin babu masu gidaje ko kuma jama'a kuma an haramta wa masunta zuwa wurin. Wurin zaman 'yan ta'adda ne, abokan su da ma'aikatansu a kasuwancin kifi.
"Wasu daga cikin mayakan ta'addancin da ke wurin an ajiye su ne kawai suna jiran umarnin shugabanninsu domin kaddamar da hari kan sojojin da ke wurin," yace.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Majiyar ta kara da cewa mayakan da yawa da suka samu rauni a ranar Lahadi sun ki zuwa asibiti domin neman lafiya saboda tsoron kada a cafke su.

Rahoto: Yadda datse layikan sadarwa ke barazana ga kasuwanci a arewa maso yamma

A wani labari na daban, kasuwanci ne a halin yanzu ke jin tsanani kan hukuncin gwamnati na datse layikan sadarwa a wasu jihohin arewa maso yamma na kasar nan kamar yadda rahotannin SB Morgan suka bayyana, TheCable ta ruwaito.

Rahotan mai taken; "Hostile reception - The impact of telephony shutdowns in North-West Nigeria," wanda aka bincike mutum 679 a makon tsakiyan watan Satumban 2021 domin duba abinda datse kafofin sadarwa suka janyo.

A ranar 3 ga watan Satumba, an bukaci hukumar sadarwa da ta bai wa kamfanonin sadarwa umarnin datse sabis a Zamfara domin shawo kan miyagun al'amuran 'yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel