Rahoto: Yadda datse layikan sadarwa ke barazana ga kasuwanci a arewa maso yamma
- Rahoton SBM ya ji ta bakin jama'a mazauna jihohin Zamfara, Katsina da Kaduna kan datse layikan sadarwa
- Kamar yadda wadanda aka ji ta bakinsu suka bayyana, sun koka da yadda kasuwancinsu suka durkushe a cikin kwanakin nan
- Amma sai dai, mazauna jihohi Zamfara da Katsina sun jinjina wa gwamnati kan yadda tsaro ya inganta a yankunansu
Kasuwanci ne a halin yanzu ke jin tsanani kan hukuncin gwamnati na datse layikan sadarwa a wasu jihohin arewa maso yamma na kasar nan kamar yadda rahotannin SB Morgan suka bayyana, TheCable ta ruwaito.
Rahotan mai taken; "Hostile reception - The impact of telephony shutdowns in North-West Nigeria," wanda aka bincike mutum 679 a makon tsakiyan watan Satumban 2021 domin duba abinda datse kafofin sadarwa suka janyo.
A ranar 3 ga watan Satumba, an bukaci hukumar sadarwa da ta bai wa kamfanonin sadarwa umarnin datse sabis a Zamfara domin shawo kan miyagun al'amuran 'yan bindiga.
Jihohi kamar Katsina da Sokoto sun bi sahun datse layikan sadarwan a wasu kananan hukumominsu, TheCable ta wallafa.
Wannan hukuncin datse layikan sadarwan a wasu jihohin ya janyo cece-kuce daga jama'a.
Daga binciken, an samu ra'ayoyin mutum 238 a Kaduna, 234 daga Katsina da kuma 207 daga Zamfara.
Abinda binciken ya samo ya bayyana cewa dukkan mazauna Zamfara ba su samun damar amfani da layikan wayoyi, kashi 13 na jama'ar Kaduna ba su samun damar amfani da layikan yayin da kashi 3 na Katsina basu samun damar amfani da layikan.
A bangaren kasuwanci, kashi 61 na wadanda aka tattauna da su a Zamfara ba su iya amfani da sabis kuma sun ce hakan ya matukar taka rawa wurin dakile al'amuran kasuwancinsu yayin da sauran suka ce illa kadan hakan yayi musu.
A Kaduna, kashi 62 daga cikin wadanda aka zanta da su ba su amfani da sabis sun ce wannan umarni bai wani takura su ba da kasuwancin, yayin da kashi 29 suka ce hakan ya matukar lalata musu kasuwanci.
A Katsina, kashi 57 na wadanda aka zanta da su kan rasa sabis sun ce umarnin ya dan taba su da kasuwancin su yayin da kashi 14 suka ce sun fuskanci matsanciyar takura da kuma matsala a kasuwancinsu.
A bangaren tsaro kuwa, kashi 43 na wadanda aka zanta da su a Zamfara sun ce harkar tsaro ta inganta tun bayan datse sabis, yayin da kashi 18 na Kaduna da kashi 14 na Katsina suka ce tsaro ya inganta a jihohin su.
Rahoton ya kara gano cewa, kasuwanci a Zamfara ne suka fi durkushewa saboda tattalin arzikin ta fiye da Kaduna da Katsina.
"A yankin da tuni ya ke fama da matsalar fatara, yanzu haka mazauna yankin na siyan abubuwa a farashi mai tsada saboda luguden da sojoji ke yi wa 'yan bindiga," rahoton yace.
"Wannan halin matsin rayuwa da ake ciki yasa muke ta kira da a hakura da datse sabis domin mazauna jihar su koma kasuwancin su kuma hukumomin tsaro su duba cigaban da aka samu.
"Daya daga cikin abubuwan da ke assasa rashin tsaro a arewa maso yamma shi ne talauci. Duk wani mataki da aka dauka wanda ya bayyana karuwar matsin rayuwa dole ne ya kasance na gajeren lokaci don kada a kara wani matsin ga jama'a.
Wani abu kuma da datse sabis shi ne rashin sanin halin da sojoji suke ciki ko kuma yadda ayyukan su ke cigaba. Labarai a yankin arewa maso yamma sun yi karanci kuma umarnin da aka bada ya na daidai da na datse kafofin yada labarai.
Daga bisani, NYSC ta ce ita ta fitar da shawarar biyan kudin fansa, za ta fara bincike a kai
A wani labari na daban, a abinda da ya janyo wa hukuma NYSC cece-kuce, ta aminta da cewa daga cikin takardun bayanai kan tsaronta ne ga ma'aikata da kuma 'yan bautar kasa aka samu wannan shawarar wacce ta matukar tada kura.
Shawarar ta bukaci duk masu hidimar kasa da kuma ma'aikata masu kaiwa da kawowa kan manyan tituna da ke da hatsari da su sanar da iyaye, 'yan uwa da abokan arziki ko kuma wadanda za su iya biyan kudin fansarsu idan an sace su.
Hukumar ta ce ta gaano cewa tabbas wannan takardar ta gama yawo a gari amma akwai wadanda babu wannan shawarar a ciki, Premium Times ta wallafa.
Asali: Legit.ng