'Yan bindiga sun sake sakin wasu dalibai 10 na kwalejin Baptist da ke Kaduna

'Yan bindiga sun sake sakin wasu dalibai 10 na kwalejin Baptist da ke Kaduna

  • Miyagun 'yan bindiga a jihar Kaduna sun sake sakin wasu dalibai 10 na makarantar Baptist High School
  • Kamar yadda shugaban CAN na jihar ya sanar, tuni aka mika daliban hannun iyayensu ranar Lahadi
  • A halin yanzu, dalibai 11 ne suka rage hannun 'yan bindigan da suka sace su a watan Yulin da ta gabata

Kaduna - Miyagun 'yan bindiga sun sake sakin wasu dalibai 10 na makarantar Bethel Baptist High School da ke Kaduna, Daily Trust ta wallafa.

Kamar yadda Joseph Hayab, shugaban kungiyar Kiristoci ta jihar Kaduna (CAN) ya sanar, an sako daliban 10 ne a ranar Lahadi.

'Yan bindiga sun sake sakin wasu dalibai 10 na kwalejin Baptist da ke Kaduna
'Yan bindiga sun sake sakin wasu dalibai 10 na kwalejin Baptist da ke Kaduna. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Hayab ya ce tuni aka mika wa iyayen yaran 'ya'yansu.

"Yan bindiga sun sake sako karin dalibai 10 na makarantar Baptist High School da rana. A halin yanzu 11 ne suka rage a hannun miyagun."

Kara karanta wannan

Sojin Najeriya sun dakile farmakin da Boko Haram suka kai sansanin soji da wasu yankunan Yobe

"Muna mika godiya ga dukkan 'yan Najeriya kan addu'o'insu da goyon bayansu. Mun sakankance cewa Ubangiji zai kubutar da sauran," yace.

Miyagun 'yan bindiga sun dira makarantar a watan Yuli inda suka yi awon gaba da sama da dalibai 100.

Sai dai, 'yan bindigan sun dinga sakin daliban kashi-kashi.

'Yan bindiga na cin karensu babu babbaka a jihohin yankin arewa maso yammacin kasar nan inda suka kware wurin shiga makarantu su kwashe dalibai.

Miyagun sun kwashe dalibai a jihohin Zamfara, Katsina kafin sun gangaro jihar Kaduna inda suka fara da makarantar gaba da sakandare.

KASU: El-Rufai ya bayyana dalilin da yasa ba zai rage kudin makaranta ba

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a ranar Asabar ya ce gwamnatin jihar ba za ta janye karin kudin makaranta da ta yi wa jami'ar jihar.

Kara karanta wannan

Bidiyon Jami'an yan sanda yayinda suka damke karya kan laifin cizon dalibin jami'a a azzakari

Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, El-Rufai ya ce gwamnatinsa ba za ta iya daukar nauyin ilimi a wannan matakin ba.

Gwamnan ya sanar da hakan a jawabin da ya yi yayin yayen dalibai na shekaru 4 da suka gabata na jami'ar jihar Kaduna (KASU) wanda aka yi a jami'ar da ke kan titin Tafawa Balewa da ke jihar.

A watan Yunin shekarar nan ne dalibai suka balle zanga-zanga kan karin kudin makarantar da gwamnatin jihar ta yi musu inda suka ce gwamnati za ta toshe hanyar da daliban jihar za su yi karatu har zuwa matakin jami'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel