KASU: El-Rufai ya bayyana dalilin da yasa ba zai rage kudin makaranta ba

KASU: El-Rufai ya bayyana dalilin da yasa ba zai rage kudin makaranta ba

  • Malam Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya ce ba zai taba janye karin kudin makarantar KASU ba
  • Gwamnan ya ce gwamnati ba ta da karfin daukar nauyin karatun jama'a har zuwa matakin jami'a, don haka ta janye tallafi
  • Ya yi kira ga iyayen dalibai da daliban da su bai wa gwamnati goyon baya ganin halin da tattalin arziki ya ke ciki yanzu

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a ranar Asabar ya ce gwamnatin jihar ba za ta janye karin kudin makaranta da ta yi wa jami'ar jihar.

Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, El-Rufai ya ce gwamnatinsa ba za ta iya daukar nauyin ilimi a wannan matakin ba.

KASU: El-Rufai ya bayyana dalilin da yasa ba zai rage kudin makaranta ba
KASU: El-Rufai ya bayyana dalilin da yasa ba zai rage kudin makaranta ba. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Gwamnan ya sanar da hakan a jawabin da ya yi yayin yayen dalibai na shekaru 4 da suka gabata na jami'ar jihar Kaduna (KASU) wanda aka yi a jami'ar da ke kan titin Tafawa Balewa da ke jihar.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Arewa maso yamma ta rikice, kiyasin mu ya na kai da kai da Afghanistan

Tushen labarin

A watan Yunin shekarar nan ne dalibai suka balle zanga-zanga kan karin kudin makarantar da gwamnatin jihar ta yi musu inda suka ce gwamnati za ta toshe hanyar da daliban jihar za su yi karatu har zuwa matakin jami'a.

Jami'ar ta daga kudin makarantar ta inda ya kai N300,000 zuwa N400,000 daga N36,000, Premium Times ta ruwaito

A yayin yayen daliban, El-Rufai ya ce jihar na bukatar hanyoyin daukar nauyin ilimin gaba da sakandare. Ya ce hakan ne yasa majalisar zartarwa ta jihar ta amince da daga kudin makaranta a dukkan makarantun gaba da sakandare na jihar.

"Wannan ya janyo cece-kuce daga iyaye da dalibai wadanda suka saba biyan kasa da N30,000 a kowacce shekara a KASU. Mun gano yadda aka saba da biyan kudin makarantan, duban yadda komai ya tashi, dala ta daga dole ne a nemo abun yi," gwamnan yace.

Kara karanta wannan

Ba zai yuwu arewacin Najeriya ta cigaba da mulki har abada ba, Shina Peller ga NEF

El-Rufai ya ce babu shakka zai tallafi ilimi a manyan makarantun jihar in har ya san cewa gwamnati za ta iya samar da abubuwan da ake bukata a makarantun.

"Ba a 1960, 1970 ko 1980 mu ke ba lokacin da gwamnati ke iya bada karatun jami'a a kyauta. Mun san cewa yanzu gwamnati a takure ta ke baya ga daliban da take kula da su a sauran matakan karatu.
"Don haka a yayin da gwamnati ke bada ilimi kyauta na shekaru 12 har zuwa aji shida na sakandare, dole ne ta samo hanyar daukar nauyin ilimin gaba da sakandare," gwamnan yace.
"Halin da tattalin arziki da rashin kudin da gwamnati ke ciki yasa bukatar hada kan gwamnati, iyaye da dalibai wurin daukar nauyin ilimin gaba da sakandare. Gwamnati ta na rokon iyaye da dalibai da su hada kai da ita domin matakin yayi aiki," El-Rufai yace.

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta dauka matakin tallafawa KASU wurin zama jami'a mai karfi.

Kara karanta wannan

Nan da shekaru 2 za a kammala wurin kiwon shanun jihar Kaduna na N10bn, El-Rufai

Mata mafarauta: A bamu wuka da nama, harsashi ba ya ratsa mu, za mu iya da 'yan bindiga

A wani labari na daban, kungiyar mafarautan Najeriya, NHC, reshen jihar Katsina da ke arewa maso yamma ta yanke shawarar taimaka wa gwamnatin jihar yaki da ta’addanci a fadin jihar.

Hajiya Ummah Dauda, mataimakiyar kwamanda janar na kungiyar, ta jagoranci sauran ‘yan kungiyar zuwa ofishin sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Muhammad Inuwa, LIB ta ruwaito.

Yayin jawabi a ofishin SAG, ACG Ummah ta bayyana cewa a cikin kungiyar mafarautan da za su iya sadaukar da ran su wurin kawo karshen ta’addanci a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel