Bidiyon Jami'an yan sanda yayinda suka damke karya kan laifin cizon dalibin jami'a a azzakari
- Jami'an yan sanda a jihar Ondo sun damke wata karya mai suna Charlie kan laifin cizon wani dalibin jami'ar Adekunle Ajasin, Akungba-Akoko a azzakari.
- An ruwaito cewa wannan abu ya faru ne ga dalibin a dakin kwanan dalibai kuma aka kira yan sanda.
- An garzaya da dalibin asibiti inda Likitoci ko kokarin ganin cewa an mayar masa da mazakutarsa
Wata karya ta shiga komar yan sanda a jihar Ondo bayan ta ciji dalibin jami'an Adekunle Ajasin, Akungba-Akoko a mazakutarsa.
Instablog9ja ta ruwaito cewa karyar mai suna Charlie ta gantsari dalibin ne a harabar wajen kwanan dalibai.
Da wuri aka garzaya da dalibin asibiti kuma mutane suka gayyaci jami'an yan sanda don su kama karyar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A bidiyon, an ga yadda yan bindiga sukayi awon gaba da karyar cikin motarsu.
Har yanzu dai ba'a san halin da yaron ke ciki ba.
Kalli bidiyon: Latsa gaba zuwa hoton karshe don ganin bidiyon
Mutane sun tofa albartakun bakinsu a kafafen ra'ayi da sada zumunta:
Abu Shuraem Marafa yace:
Marassa lafiyanmu nagida danawaje Allah kabasu lfy
Usman Musa Adam Alkaulahee yace:
Su matsashi yabada bayanai turoshi akayi
Aliyu Lawal Namadan yace:
Kai wllh abun dariya abun tausayi,
Nigeria kasarmu ta gado
Magaji Abdulhakim yace:
Duk cikin aiki ne sai anbiya kudin beli
Aliyu Bala Ibraheem yace:
Tab lallai akwai matsala babba azzakari kuma???
Sunusi Suraja Adamu Adam yace:
To zaro azzakarin yayi waje tagani takai Hari kokuwa ya abun yakene.
Asali: Legit.ng