Daga bisani, NYSC ta ce ita ta fitar da shawarar biyan kudin fansa, za ta fara bincike a kai

Daga bisani, NYSC ta ce ita ta fitar da shawarar biyan kudin fansa, za ta fara bincike a kai

  • Daga bisani, hukumar NYSC ta amsa cewa littafin shawarwari kan tsaronta ne ke kunshe da lamarin da ya janyo cece-kuce
  • Hukumar ta saki wasu shawarwari kan cewa masu kaiwa da kawowa a miyagun tituna su sanar da 'yan uwa su tanadi kudin fansa
  • Mai magana da yawun hukumar, Adenika Adeyemi, ta ce hukumar ta fara bincike kan wannan lamarin

A abinda da ya janyo wa hukuma NYSC cece-kuce, ta aminta da cewa daga cikin takardun bayanai kan tsaronta ne ga ma'aikata da kuma 'yan bautar kasa aka samu wannan shawarar wacce ta matukar tada kura.

Shawarar ta bukaci duk masu hidimar kasa da kuma ma'aikata masu kaiwa da kawowa kan manyan tituna da ke da hatsari da su sanar da iyaye, 'yan uwa da abokan arziki ko kuma wadanda za su iya biyan kudin fansarsu idan an sace su.

Kara karanta wannan

Duk da musantawa, Bidiyon NYSC na shawarta masu hidimar kasa su tattara kudin fansarsu da kansu

Hukumar ta ce ta gaano cewa tabbas wannan takardar ta gama yawo a gari amma akwai wadanda babu wannan shawarar a ciki, Premium Times ta wallafa.

Daga bisani, NYSC ta ce ita ta fitar da shawarar biyan kudin fansa, za ta fara bincike a kai
Daga bisani, NYSC ta ce ita ta fitar da shawarar biyan kudin fansa, za ta fara bincike a kai. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Mai magana da yawun hukumar NYSC, Adenika Adeyemi a wani sako da ta tura wa Premium Times a ranar Juma'a ya ce tuni hukumar ta fada bincike kan lamarin.

Wannan martanin ya biyo bayan jaddadawan da wasu jaridu suka dinga tare da dauko hotuna da bidiyon wuraren da aka yi wannan rubutun.

Hakan yasa jama'a suka dinga mamaki tare da son sanin hikimar wannan shawarar inda wasu kuwa ke cewa Najeriya ta kamo hanyar tabarbarewa.

A wani martani guntu da Adeyami ta yi, ta ce: "Mun gano cewa kwafin wannan takardar ta gama gari. Muna bincike a kai."

Kara karanta wannan

Ina tabbatar muku za'a hukunta tubabbun yan Boko Haram: Kwamandan Operation Hadin kai

Da yawa daga cikin masu sukar Buhari su kan lallaɓa Villa diɓar 'jar miya'

A wani labari na daban, Femi Adesina, mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yada labarai, ya ce wasu daga cikin manyan masu caccakar shugaban kasan a fili suna lallabawa Aso Rock domin cin abincin dare da shi.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, mai magana da yawun shugaban kasan ya sanar da hakan ne yayin tsokaci kan komen da Femi Fani-Kayode yayi zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

A makon da ya gabata bayan shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC na kasa kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya gabatar da shi a gaban Buhari a gidan gwamnatin tarayya da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng