Kaduna: 'Yan bindiga sun kai farmaki coci, sun sheke mai bauta

Kaduna: 'Yan bindiga sun kai farmaki coci, sun sheke mai bauta

  • 'Yan bindiga dauke da miyagun makamai sun kai farmaki cocin ECWA da ke Gavaciwa a Kachia
  • A take suka harbe mai bauta daya tare da yi wa sauran ruwan wuta wanda yayi sanadiyyar raunata su
  • Samuel Aruwan, ya tabbatar da aukuwar harin tare da mutuwar mutum 1 inda yace sauran suna asibiti

Kachia, Kaduna - 'Yan bindiga sun kutsa cocin Evangelical Church of Winning All (ECWA) wacce ke Gavaciwa a karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna a ranar Lahadi inda suka sheke mai bauta 1.

Daily Trust ta ruwaito cewa, 'yan bindigan dauke da miyagun makamai sun fada cocin yayin da ake tsaka da bauta.

Kaduna: 'Yan bindiga sun kai farmaki coci, sun sheke mai bauta
Kaduna: 'Yan bindiga sun kai farmaki coci, sun sheke mai bauta. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya tabbatar da harin inda ya ce 'yan bindigan sun kashe wani mutum mai suna Nasiru Abdullahi da ke Gobirawan Kamacha a Bina da ke karamar hukumar Igabi ta jihar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro 17 yayin harin Sokoto, Ɗan Majalisa

Ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya kushe harin kuma ya jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu, TheCable ta wallafa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwamishinan ya ce, "Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya kushe harin da aka kai wa masu bauta a cikin coci a safiyar Lahadi.
"Hukumomin tsaron sun sanar da gwamnati cewa harin ya faru ne a cocin ECWA da ke Gabaciwa a karamar hukumar Kachia.
“Kamar yadda rahoto ya bayyana, an rasa rai daya, wasu masu bautar sun jigata yayin da aka garzaya da su asibiti.
"Jami'an tsaron na cigaba da samun karin bayani wanda gwamnatin ta ce za ta sanar da jama'a bayan an kammala.
“Gwamnan ya bayyana takaicinsa kan al'amarin wanda ya kwatanta da tsabar shaidanci. Ya kara da cewa kai wa masu bauta hari hanya ce ta zagon kasa ga addinai.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe mutane biyu, sun yi garkuwa da malami a Kaduna

“Gwamnan ya jajanta wa cocin ECWA da iyalan wadanda suka rasu kuma ya yi addu'ar rahama ga wanda ya rasu."

Ya ce gwamnan ya umarci hukumar bada tallafin gaggawa da ta duba yankin tare da samar da kayan rage radadi ga jama'ar da ke fama da raunika.

Datse sadarwa: 'Yan bindiga na amfani da layikan Nijar wurin kai farmaki, Dan majalisa

A wani labari na daban, 'yan bindiga suna yin amfani da kafofin sadarwa na jamhuriyar Nijar wurin kai farmaki kamar yadda Aminu Almustapha Gobir, dan majalisa mai wakiltar mazabar Sabon Birni ta arewa a majalisar jihar Sokoto.

Daily Trust ta ruwaito cewa, daga cikin hanyoyin magance matsalolin 'yan fashin bindiga, gwamnatin Najeriya ta datse dukkan hanyoyin sadarwa a jihohin Sokoto, Zamfara da Katsina.

Hakan an gano cewa ya datse sadarwa tsakanin 'yan bindigan da masu kai musu bayanai. Amma a matsayin hanyar cigaba da aiwata ta'asa, 'yan fashin sun koma amfani da kafofin sadarwa na kasashe da ke makwabtaka da ke da Najeriya ta Sokoto.

Kara karanta wannan

Gobara ta yi kaca-kaca da Hedkwatar hukumar NPA, dukiyoyi sun kone kurmus

Asali: Legit.ng

Online view pixel