Fusatattun 'yan fansho sun garkame SSG na Ogun kan rike N68bn na garatutinsu

Fusatattun 'yan fansho sun garkame SSG na Ogun kan rike N68bn na garatutinsu

  • Fusatattun 'yan fansho a jihar Ogun sun garkame SSG da sauran ma'aikata inda suka hana su shiga ofisoshinsu
  • 'Yan fanshon na zargin gwamnatin jihar Ogun da rike musu N68 biliyan kudi garatuti na kusan shekaru goma
  • Tsofaffin ma'aikatan suna bukatar a biya su kudadensu, a daina jinkirin biyan fansho kuma a dawo biyansu ta kananan hukumominsu

Abeokuta, Ogun - Fusatattun 'yan fansho na jihar Ogun a ranar Laraba sun rufe sakateriyar jihar inda ofishin gwamnan ya ke da zanga-zanga saboda kin biyansu kudinsu har N68 biliyan kusan shekaru goma kenan da suke bin gwamnatin.

Daily Trust ta ruwaito cewa, 'yan fanshon da ke karkashin kungiyar karamar hukuma sun mamaye manyan kofofi 2 na sakateriyar da ke Oke-Mosan a Abeokuta inda suka hana SSG Tokunbo Talabi da sauran ma'aikatan shiga tsawon sa'o'i hudu.

Kara karanta wannan

Jerin manyan yan adawan gwamnatin Buhari 4 da suka mutu a shekarar nan

Fusatattun 'yan fansho sun garkame SSG na Ogun kan rike N68bn na garatutinsu
Fusatattun 'yan fansho sun garkame SSG na Ogun kan rike N68bn na garatutinsu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Masu zanga-zangar sun tafi dauke da takardu wadadna aka yi rubuce-rubuce daban-daban domin nuna fushinsu kan lamarin.

A watan Yuni, mambobin kungiyar LOGPAN sun fita zanga-zanga domin nuna takaicinsu kan abinda ke faruwa, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin jawabi ga manema labarai, shugaban kungiyar, Sikiru Ayilara, ya jajanta abinda ya kwatanta da rashin tausayin dan Adam da gwamnatin Abiodun ke nuna musu.

Ya zargi Abiodun da kasa cika alkwarinsa ga 'yan fansho inda ya ce har a halin yanzu akwai wadanda ke karbar N3,000 a matsayin kudin fansho.

Ya lissafo bukatunsu da suka hada da rashin biyan garatutinsu, biyan fansho ba kan lokaci ba, rashin kara musu yawan kudin fansho da kuma nuna banbanci tsakanin mambobin kungiyarsu.

Ayilara ya jaddada cewa, ba daidai ba ne gwamnatin jihar ta dinga biyan kudin fanshonsu ta ma'aikatar kudi a maimakon ofis din karamar hukuma.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun afkawa coci ana cikin ibada, sun kashe mutum 1, sun sace 3

A yayin martani ga 'yan fanshon, SSG Tokunbo Talabi ya yi kira garesu da su kara hakuri da gwamnatin inda ya ce gwamnatin ta na cikin halin matsi.

Ya tabbatar da cewa, gwamnati za ta duba dukkan bukatun 'yan fanshon.

Hotunan shugaban EFCC yayin da ya gurfana a gaban kotu domin bada shaida

A wani labari na daban, Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ya bayyana gaban Mai shari'a Sedoton Ogunsanya na babbar kotun Ikeja da ke jihar Legas a ranar Talata.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya bayyana ne domin bada shaida a matsayinsa na babbar shaidar masu kara a wata harkallar mai da aka waskar da kudi har naira biliyan 1.4.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Nadabo Energy da shugabanta, Abubakar Peters, kan zarginsu da karbe kudi har biliyan 1.4 daga gwamnatin tarayya a matsayin tallafin mai tare da samun wasu takardun bogi.

Kara karanta wannan

Makiyayi da shugaban Fulani sun sheka lahira bayan 'yan bindiga sun kai farmaki Kaduna

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: