Kano: Gwamnati ta hana nuna fina-finai masu nuna shaye-shaye da garkuwa da mutane

Kano: Gwamnati ta hana nuna fina-finai masu nuna shaye-shaye da garkuwa da mutane

  • Hukumar tace fina-finan jihar Kano ta dakatar da nuna fina-finai dake dauke da ayyukan masha’a
  • Hukumar ta hana nuna fina-finai dauke da garkuwa da mutane, shaye-shaye da kwatar wayoyi a jihar
  • Sakataren hukumar, Ismaila Naaba Afakallah ya sanar da wannan umarnin wanda ya ce zai taimaka wurin hana ta’addanci

Jihar Kano - Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta hana nuna fina-finai da kuma sayar da fina-finan da suke dauke da garkuwa da mutane, shaye-shaye da kuma kwace wayoyi a fadin jihar kamar yadda LIB ta ruwaito.

Sakataren hukumar, Ismaila Naaba Afakalla ne ya sanar da wannan umarnin inda ya ce anyi hakan ne don dakatar da yara daga koyon ta’addanci a jihar.

Kano: Gwamnati ta hana nuna fina-finai masu nanu shaye-shaye da garkuwa da mutane
Taswirar Jihar Kano. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta ce ba ta da sha'awar kunyata masu daukar nauyin ta'addanci

Hukumar ta dakatar da irin shirye-shiryen don taimakon tarbiyyar yara

Kamar yadda LIB ta ruwaito, Afakalla ya ce:

“Daga yanzu, mun hana nuna fina-finai dake dauke da garkuwa da mutane, shaye-shaye da kuma kwacen wayoyi a fadin jihar.”

Afakallah ya bayyana cewa hakan zai taimaka wurin dakatar da hanyoyin da kananun yara za su yi koyi da ta’addanci.

Inda ya kara da cewa matsawar kananun yara sun ga jarumi yana aikata hakan za su iya koyi da shi.

Ya kara da cewa:

“Ba ko wanne karamin yaro ne zai iya gane cewa shirin fim bane. Yaro zai iya dauka da gaske lamarin yake faruwa don haka ya tafi ya aiwatar. Don haka wajibi ne a dakatar kafin ya auku."

A raba mu, ya ce na cika mugun ci, har rufe kicin yake yi da dare, Firdausi ta yi karar mijinta Haruna a kotu

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Zata Sha Ƙasa a Zaɓen 2023 Matukar Ta Tsayar da Ɗan Arewa, Jigon PDP

A wani labarin daban, a ranar Litinin wata Firdausi Sulaiman mai shekaru 23 ta maka mijinta, Haruna Haruna a gaban kotun musulunci da ke zama a Magajin Gari a Kaduna tana bukatar a raba auren su da shi saboda yadda yake dukanta kamar gangar tashe sakamakon mungun cin abincin ta.

Kamar yadda NewsWireNGR ta bayyana, a korafin da ta yi wa Kotu, Firdausi wacce take zama a Rigasa dake Kaduna ta ce har rufe kicin Haruna yake yi da dare.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel