Jam'iyyar PDP Zata Sha Ƙasa a Zaɓen 2023 Matukar Ta Tsayar da Ɗan Arewa, Jigon PDP

Jam'iyyar PDP Zata Sha Ƙasa a Zaɓen 2023 Matukar Ta Tsayar da Ɗan Arewa, Jigon PDP

  • Tsohon kakakin shugaban ƙasan da ya gabata, Doyin Okupe, ya gargaɗi jam'iyyar PDP kada ta kai tikitin shugaban ƙasa arewa
  • Jigon babban jam'iyyar hamayya ta ƙasa yace jam'iyyar ka iya rasa damarta na kwace mulki daga hannun APC matukar ta yi haka
  • A cewarsa bai dace ba a maye gurbin shugaban ƙasa Buhari da wani daga yankin arewa ba

Abuja - Tsohon kakakin shugaban ƙasa kuma jigon PDP, Doyin Okupe, ya gargaɗi PDP kan duk wani shiri na hana yankin kudu tikitin takara a zaɓen 2023, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Okupe ya bayyana cewa akwai babar alamar da ke nuna cewa jam'iyyar na shirye-shiryen kai tikitin takara yankin arewacin Najeriya a zaɓen 2023.

Yace baban rashin adalci ne, kuma ba dai-dai bane PDP ta tsayar da ɗan takara daga yankin arewa a 2023.

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen dan majalisar arewa ya bayyana dalilin da ya sa APC ke zawarcin Jonathan, ya yi magana akan kudirin Tinubu

Jigon PDP ya yi tsokaci game da rikin tsarin karɓa karba a wurin taron manema labarai, a birnin tarayya Abuja.

Doyin Okupe
Jam'iyyar PDP Zata Sha Ƙasa a Zaɓen 2023 Matukar Ta Tsayar da Ɗan Arewa, Jigon PDP Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Vanguard ta ruwaito Okupe yace:

"Ficewar da wasu ke yi daga PDP ba shi da alaƙa da rikicin jam'iyyar, sauya sheka wani abu ne da ya saba faruwa da zaran babban zaɓe ya kusanto."
"Amma lamarin tsarin karɓa-karba ba shi da wata matsala da masu sauya sheƙa saboda ba da jimawa ba kwamitin da aka kafa zai kammala aikinsa ya mika rahoto."
"Duk da haka akwai manyan alamun PDP na shirin kai tikitin takara arewa. Tsarin mulkin karba-karba babban ginshiki ne na dai-daito a ƙasa, kuma PDP ta fara tsarin ne a shekarar 1998 da tsammanin cewa ita zata cigaba da mulkin ƙasa."

APC ta kwace mulki a 2015

Okupe ya kara da cewa lokacin da jam'iyyar PDP ta rasa mulki a 2015, ɗan kudu ne ke kan mulki.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Manyan mukamai da Fani-Kayode zai iya samu a matsayin tukwicin sauya sheka zuwa APC

"Da ace PDP ba ta faɗi zaɓe ba zai kammala mulki a 2019, daga nan sai a maida shugaban ƙasa ya koma yankin arewa."
"Zuwa 2023 APC ta mulki ƙasa na tsawon shekara 8 da shugaban ƙasa daga Arewa, saboda haka kwata-kwata bai dace ba a maye gurbin ɗan arewa da ya shafe shekaru 8 a kan mulki da wani ɗan arewan ba.

Gwamnonin PDP sun maida martani

A wani labarin na daban kuma Gwamnonin PDP Sun Maida Martani Kan Ikirarin Gwamnan da Ya Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar APC

Kungiyar gwamnonin PDP, (PDP-GF), tace gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, ya ci amanarsu a zaɓen 2019.

Gwamnonin sun faɗi haka ne yayin martani kan tsoma bakin Umahi a abinda ya shafe su da jam'iyyar hamayya PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel