Jerin gwamnonin Najeriya da suka dage sai jihohi sun karbi harajin VAT da wadanda suka yi watsi da yunkurin

Jerin gwamnonin Najeriya da suka dage sai jihohi sun karbi harajin VAT da wadanda suka yi watsi da yunkurin

  • Gwamnonin kudu sun yi wani taro a Enugu don tattauna muhimman batutuwa da yankin ke fuskanta
  • Daya daga cikin mahimman batutuwan da suka tattauna shine na karbar harajin VAT
  • Yayinda wasu jihohi ke adawa da FIRS kan karbar haraji wasu na goyon bayan gwamnatin tarayya

Najeriya - A ranar Alhamis, 16 ga Satumba, gwamnoni a Kudancin Najeriya sun yi wani taro a Enugu don tattauna muhimman batutuwa da yankin ke fuskanta.

Daya daga cikin mahimman batutuwan da suka tattauna shine na karbar harajin VAT.

Hukumar tattara kudaden shiga ta tarayya (FIRS) ce ta saba karbar harajin VAT har zuwa kwanan nan da gwamnatin jihar Ribas ta kalubalanci hukumar ta tarayya.

Jerin gwamnonin Najeriya da suka dage sai jihohi sun karbi harajin VAT da wadanda suka yi watsi da yunkurin
Jerin gwamnonin Najeriya da suka dage sai jihohi sun karbi harajin VAT da wadanda suka yi watsi da yunkurin Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Asali: Facebook

Gwamnatin jihar Legas ta bi sahu yayin da gwamnoni ke neman kwace ikon karbar harajin VAT daga gwamnatin tarayya. Yanzu haka lamarin yana kotun daukaka kara bayan da gwamnatin jihar Ribas ta yi nasara a matakin babbar kotun tarayya.

Kara karanta wannan

Yadda 'Yan Bindiga Suka Ƙi Karbar Kuɗin Da Aka Kai Musu Don Fansar Mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da gwamnoni da yawa ke goyan bayan jihohi su rika karbar harajin VAT, akwai kuma wasu kalilan da ke ganin ya kamata FIRS ta ci gaba da karbar harajin.

A taron gwamnonin kudancin kasar, rahotannin kafafen yada labarai sun bayyana cewa sun hadu sun goyi bayan karbar VAT daga jihohi.

Sai dai kuma, Legit.ng ta lura cewa wasu gwamnoni ba su halarci taron ba, sun zabi tura mataimakan su.

Idan aka yi la’akari da wannan yunƙurin, yana da wahala a iya tantance idan da gaske duk gwamnonin kudancin ƙasar suna goyon bayan jihohi su harajin VAT.

Hakanan yana da mahimmanci a lura cewa daya daga cikin gwamnonin kudancin, David Umahi na Ebonyi, a baya ya goyi bayan FIRS don ci gaba da tattara VAT.

Ga jerin gwamnonin da suka goyi bayan jahohi su karbi harajin VAT, maimakon FIRS:

Kara karanta wannan

'Yan Majalisa na Kudu sun yi taro a gidan Ekweremadu kan ceto Nnamdi Kanu

1. Oluwarotimí Akeredólu (SAN) - gwamnan jihar Ondo

2. Ifeanyi Ugwuanyi - gwamnan Enugu

3. Nyesom Wike - gwamnan jihar Rivers

4. Emmanuel Udom - jihar Akwa Ibom

5. Babajide Sanwo -Olu - jihar Legas

6. Ifeanyi Okowa na Delta - jihar Delta

7. Adegboyega Oyetola – jihar Osun

8. Douye Diri - jihar Bayelsa

9. Dapo Abiodun - Jihar Ogun

Kamar yadda jaridar The Sun ta ruwaito, gwamnoni tara ne suka hallara yayin da bakwai suka tura mataimakan su daga cikin jihohi 17 na yankin. Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, ba ya nan kuma bai aiko da wani wakili ba.

Gwamnoni da ba sa goyon bayan jihohi su karbi VAT

Yahaya Bello

Kamar dai Ebonyi, gwamnatin jihar Kogi ta ce ba za ta saka kanta a cikin shirin karbar VAT ba kamar yadda gwamnatocin Legas da Ribas suka fara ba.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari ya wanke Arewa, ya yi wa Gwamna Wike kaca-kaca a kan rikicin harajin VAT

Yunkurin da jihohin biyu suka yi ya samu adawa daga jihar Kogi ta hannun kwamishinan yada labarai, Kingsley Fanwo, inji rahoton The Punch.

Muhammad Inuwa Yahaya

Haka kuma, gwamnatin jihar Gombe tana adawa da karbar harajin VAT da jihohi ke son yi.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa kwamishinan kudi da raya tattalin arzikin jihar, Muhammad Magaji, ya roki Legas da Ribas da su kasance masu tsaron ‘yan uwansu ta hanyar bayar da gudunmawa ga cibiyar.

Hadimin Buhari ya wanke Arewa, ya yi wa Gwamna Wike kaca-kaca a kan rikicin harajin VAT

A wani labarin, a ranar Litinin, 13 ga watan Satumba, 2021, Ajuri Ngelale ya caccaki gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike kan matsayarsa a game da batun VAT.

Ajuri Ngelale wanda shi ne ke taimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen hulda da jama’a ya soki kabilancin da gwamnan yake nuna wa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kotun daukaka kara ta hana jihar Legas da Rivers karbar kudin harajin VAT

Jaridar Punch ta rahoto Ajuri Ngelale yana cewa gwamnatin tarayya ba ta daukar dukiyar Neja-Delta masu arzikin mai, ta kai wa Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel