Hadimin Buhari ya wanke Arewa, ya yi wa Gwamna Wike kaca-kaca a kan rikicin harajin VAT
- Ajuri Ngelale ya yi bayani game da yadda ake tattara harajin VAT a kasar nan
- Hadimin Shugaban kasar ya soki matsayar Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike
- Ngelale yace ba daidai ba ne a ce gwamnatin tarayya tana ta ci da gumin jihohi
Abuja - A ranar Litinin, 13 ga watan Satumba, 2021, Ajuri Ngelale ya caccaki gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike kan matsayarsa a game da batun VAT.
Ajuri Ngelale wanda shi ne ke taimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen hulda da jama’a ya soki kabilancin da gwamnan yake nuna wa.
Jaridar Punch ta rahoto Ajuri Ngelale yana cewa gwamnatin tarayya ba ta daukar dukiyar Neja-Delta masu arzikin mai, ta kai wa Arewacin Najeriya.
Meyasa FIRS take karbar haraji?
Ngelale ya yi karin-haske game da yadda gwamnatin tarayya take tattara harajin VAT a jihohi 36. Jaridar ta rahoto shi yana bayyana hikimar kafa FIRS.
Mista Ngelale yake cewa FIRS tana karbar VAT a jihohin kasar nan ne domin a samu saukin kasuwanci, akasin abin da wasu gwamnoni ke neman yi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hadimin shugaban kasar ya yi wannan bayani a lokacin da aka yi hira da shi a shirin ‘Sunrise Daily’ a gidan talabijin na Channels a safiyar ranar Litinin.
Mai ba shugaban Najeriyar shawara yace idan aka bar gwamnoni su rika karbar VAT, ‘yan kasuwa za su rika biyan harajin kayan masurufi fiye da sau daya.
Ba kudin jihohi ba ne
“A 2020, Najeriya ta samu N1.5tr daga VAT. Mun samu 60% na VAT daga tashoshinmu, kamar yadda aka sani tashoshi ba mallakar gwamnatin jihohi ba ne. Saboda haka ba kudin shigarsu ba ne; harajin gwamnatin tarayya ne.”
“Bayan Legas, sai Abuja da ke samun N202bn, dalilin haraji sosai shi ne nan ne birnin tarayya, inda ake da ma’aikatu da hukumomin gwamnati.”
“Idan muna nuna wadannan haraji na jihohi ne, gwamnatin tarayya take karba, tana raba wa jihohin, ana neman zuzuta abin ne.”
FIRS za tayi asara
A makon nan aka ji cewa kudin da ke shiga asusun Gwamnatin Tarayya zai yi kasa da Naira biliyan 96 idan aka bar jihohi da alhakin karbar harajin VAT.
Rahotanni suna cewa babu mamaki a sallami wasu ma'aikatan da ke FIRS saboda karancin kudin shiga, ko kuma akalla a rage wa jami'an alawus da albashinsu.
Asali: Legit.ng