Yadda 'Yan Bindiga Suka Ƙi Karbar Kuɗin Da Aka Kai Musu Don Fansar Mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara

Yadda 'Yan Bindiga Suka Ƙi Karbar Kuɗin Da Aka Kai Musu Don Fansar Mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara

  • 'Yan bindigan da suka sace mahaifin kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara sun ki karbar kudin fansa
  • Wani hadimin kakakin majalisar ya bayyana yadda wani tsohon kwamishina a jihar ya jagoranci tattaunawar
  • Majiyar ta ce da farko an nemi Kachalla ya yi sulhun amma daga bisani suka kai kudin da kansu sansanin Turji amma aka ki amsa

'Yan bindiga a jihar Zamfara sun ki karbar kudin fansar da kakakin majalisar jihar Zamfara, Nasir Magarya ya bada domin kubutar da mahaifinsa daga hannunsu.

Premium Times ta ruwaito cewa an sace mahaifin Mr Magarya ne tare da wasu mutane biyar a wata Agusta yayin wani hari da aka kai kauyen Magarya a karamar hukumar Zurmi.

Yadda 'Yan Bindiga Suka Ƙi Karbar Kuɗin Da Aka Kai Musu Don Fansar Mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara
Taswirar Jihar Zamfara. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Da duminsa: Majalisar jihar Kano ta amince da bukatar Ganduje ta karbo bashin N4bn

Rahotanni sun ce wasu jami'an gwamnati sun tuntubi shugaban 'yan bindiga, Halilu Kachalla, ya taimaka musu wurin tattaunawa da 'yan bindigan da ke tsare da mahaifin kakakin majalisar.

Wani hadimin kakakin majalisar ya shaidawa Premium Times cewa wasu jami'an karamar hukumar Shinkafi ne suka gayyaci Kachalla domin ya taimaka.

Ya ce magoya bayan kakakin majalisar a kananan hukumomin Zurmi da Shinkafi suma sun tuntubi Kachalla nan take bayan sace mutanen.

'Yan bindigan sun ki karbar kudin fansa

Wani babban hadimin kakakin majalisar, wanda ya nemi a boye sunansa ya tabbatarwa Premium Times cewa wasu hadiman kakakin majalisar sun bayar da kudin da 'yan bindigan suka tambaya.

Ya ce:

"Wani tsohon kwamishina dan Zurmi ne ke kan gaba wurin tattaunawa da 'yan bindigan. Halilu Kachalla ya yi iya kokarinsa amma yana samun matsala da mafi yawancin 'yan bindigan jihar don suna ganin yana kusantar gwamnati da yawa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace wani limamin Katolika, sun kashe mutane 11 a jihar Kaduna

"Don haka, tsohon kwamishinan ya fadawa kakakin majalisar cewa su biya fansar da kansu tunda tattaunawar da Kachalla ke yi da su bata yi nasara ba."

Amma majiyar bai ambaci adadin kudin da aka biya ba

Ya ce:

"Abin da na sani shine wasu mutanen mu a Shinkafi da Zamfara sun kai kudi sansanin Turji amma ba su same shi (Turjin) ba. Sun tattaunawa babban kwamandansa, Dan Bukkolo, amma ya ce musu an umurci su koma da kudin."

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan 'yan bindigan sun kona gidan kakakin majalisar da na kawunsa da mahaifinsa a kauyen Magarya.

An gaza ji ta bakin mai magana da yawun kakakin majalisar, Mustafa Kaura, saboda rashin wayar sadarwa a jihar.

'Yan bindiga sun afka ofishin ƴan sandan Zamfara, sunyi kisa, sun sace bindigu AK-47 masu yawa

A wani labarin daban, wasu ɓata gari da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun kai hari ofishin yan sanda a Zamfara sun kashe jami'in ɗan sanda ɗaya, rahoton SaharaReporters.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun banka wuta gidan Kakakin majalisar wakilan jihar Zamfara

Yan bindiga sun kuma kashe wani shugaban ƴan banga da wasu mutane biyu a garuruwan Nahuce da Gidan Janbula a ƙaramar hukumar Bungudu.

Har wa yau, ƴan bindigan sun yi awon gaba da mutane hudu yayin da suka kawo harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel