'Yan Majalisa na Kudu sun yi taro a gidan Ekweremadu kan ceto Nnamdi Kanu

'Yan Majalisa na Kudu sun yi taro a gidan Ekweremadu kan ceto Nnamdi Kanu

  • 'Yan majalisar tarayyar Nigeria na yankin kudu maso gabas sun yi taro kan batun Nnamdi Kanu
  • An yi taron ne a gidan tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa Mr Ike Ekweremadu
  • 'Yan majalisar sun ce manufar taron shine kafa kwamiti don ganin yadda za a wareware matsalar Kanu a siyasance

'Yan majalisar tarayyar na yankin kudancin Nigeria sun kafa kwamiti da za ta bullo da hanyoyin da za a bi domin ceto shugaban kungiyar masu neman kafa Biafra, wato Nnamdi Kanu da a yanzu ya ke tsare, The Punch ta ruwaito.

Hakan na cikin sakon bayan taro ne da kwamitin ta fitar bayan taronta a gidan tsohon mataimakin majalisar dattijai, Ike Ekweremadu a ranar Laraba a cewar rahoton na The Punch.

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane sun mamaye kauyen Abuja, sun sace matan aure 2

'Yan Majalisa na Kudu sun yi taro a gidan Ekweremadu kan ceto Nnamdi Kanu
Shugaban Kungiyar IPOB, Mazi Nnamdi Kanu. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Sakon bayan taron da dukkan 'yan majalisar kudu na yankin suka ratabba wa hannu, ta yi bayanin cewa an yi taron ne 'don tattaunawa kan batun Mazi Nnamdi da kuma yadda za a warware matsalar.'

Ta ce:

"Don haka, mun yanke shawarar kafa kwamiti da za ta gana da masu ruwa da tsaki, gwamnatin tarayya da hukumomin da abin ya shafa domin ganin an samu sulhu a siyasance. Za mu rika sanar da al'ummar Ibo abin da ke faruwa.
"Muna kira ga mutanen mu kada su bari wani ya yi amfani da su ya lalata yankin kudu maso gabas. An gina sabuwar kudu maso gabas bayan yakin basasa ne ta hanyar jajircewa da sadaukarwar mutanenmu wadanda zuciyarsu bata karaya ba."

'Yan majalisar sun yi Allah wadai da asarar rayyuka da dukiyoyi da hana rubuta jarrabawa a makarantun yankunan kudu maso gabas da sunan tilasta zaman gida da kungiyar IPOB ke yi.

Kara karanta wannan

Kwamandan NDA ya yi wa majalisa bayanin halin da ake ciki kan harin 'yan bindiga a NDA

'Yan IPOB sun tare motar burodi sun sace dukkan abin da ke ciki, sun ƙona motar

A wani labari daban, wasu mutane da ake zargin mambobin haramtaciyar kungiyar masu neman kafa kasar Biafara, IPOB, sun tare wata motar burodi a Enugu sun sace burodin sannan suka bankawa motar wuta a safiyar ranar Talata.

Lamarin ya faru ne a Emene, bayan garin babban birnin Enugu, a ranar da aka umurci mazauna garin su zauna a gida don nuna goyon baya ga Nnamdi Kanu, shugaban IPOB, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel