Abun bakin ciki: Shugabar NBA Abuja, Hauwa Shekarau ta rasu bayan yar gajeriyar rashin lafiya

Abun bakin ciki: Shugabar NBA Abuja, Hauwa Shekarau ta rasu bayan yar gajeriyar rashin lafiya

  • Shugabar kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) reshen Abuja, Hauwa Shekarau, ta rigamu gidan gaskiya
  • Hauwa Shekarau ta rasu ne a ranar Laraba, 15 ga watan Satumba, bayan ta yi fama da 'yar gajeriyar rashin lafiya
  • Sakataren NBA reshen Abuja, Prince Adetosoye ne ya sanar da labarin mutuwar tata

Kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) reshen Abuja ta rasa shugabarta, Hauwa Shekarau a ranar Laraba, 15 ga watan Satumba.

A cewar sakataren NBA reshen Abuja, Prince Adetosoye, Hauwa ta rasu bayan ta yi fama da gajeriyar rashin lafiya, jaridar Punch ta rahoto.

Abun bakin ciki: Shugabar NBA Abuja, Hauwa Shekarau ta rasu bayan yar gajeriyar rashin lafiya
Abun bakin ciki: Shugabar NBA Abuja, Hauwa Shekarau ta rasu bayan yar gajeriyar rashin lafiya Hoto: dateline.ng
Asali: UGC

Sanarwar da Adetosoye ya fitar kan wannan babban rashi ya zo kamar haka:

“Cike da bakin ciki da nauyin zuciya nake sanar da rasuwar shugabarmu, wacce ta rasu da safiyar yau, 15 ga Satumba 2021 bayan gajeriyar rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta gargadi Yarbawa kan hada kai da kungiyoyin ta'addanci

"Zan yi karin bayani game da tsare-tsare da shirye-shiryen jana'izarta daga baya."

Hauwa ta kasance fitacciyar mai fafutukar jinsi, mai fafutukar kare hakkin dan adam, kwararriyar mai shiga tsakani kuma mai sasantawa, Sahara Reporters ta ruwaito.

Ta kuma kasance kwararriyar lauya da ta shafe sama da shekaru 25 tana aikin goyan bayan kira ga manufofin kare hakkin ‘ya’ya mata da yara da bayar da shawarwari, sasanta rikici, bincike na zamantakewa da sauransu.

Dalibar da ta kammala karatun digiri a jami’ar Ahmadu Bello, Zariya ita ce shugabar kungiyar lauyoyin mata ta kasa da kasa (FIDA Nigeria) a tsakanin shekarar 2012 zuwa 2015, inda ta dauki nauyin bayar da jagoranci ga kwararriyar kungiyar wacce ke da rassan jihohi a duk fadin Najeriya.

A wani labari na daban, rundunar sojin saman Najeriya (NAF) a ranar Alhamis, 16 ga watan Satumba ta ce ta fara gudanar da bincike kan zargin barin wuta da wani jirginta ya yi kan farar hula a jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Dan Majalisar Tarayya Ya Rigamu Gidan Gaskiya, Majalisa Ta Tafi Hutu Saboda Jimami

Air Commodore Edward Gabkwet, mai magana da yawun NAF, ya bayyana a cikin wata sanarwa da aka aikewa Legit.ng.

Ya ce rahoton farko da ya karyata hatsarin ya ta'allaka ne a kan bayanan farko da rundunar sojin saman ta samu, wanda ke cewa jirgin yakin ya jefa bama-bamai ne a kan fararen hula.

Asali: Legit.ng

Online view pixel