Rundunar sojin saman Najeriya ta fara bincike kan barin wuta da jirgin yaki ya yi kan fararen hula a Yobe
- Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta fara gudanar da bincike kan harin da ake zargin jirgin sojinta ya kai tare da kashe fararen hula a garin Buhari da ke karamar hukumar Yusufarin jihar Yobe
- Da farko dai NAF ta musanta faruwar lamarin, amma a ranar Alhamis ta fitar da wata sanarwa tana bayyana kuskuren da ya faru har aka samu wannan hatsari
- Ta bayyana cewa jiragen sojin na shawagi ne yankin Kogin Kamadougou Yobe don tattara bayanan sirri kan ayyukan kungiyoyin Boko Haram da ISWAP
Yobe - Rundunar sojin saman Najeriya (NAF) a ranar Alhamis, 16 ga watan Satumba ta ce ta fara gudanar da bincike kan zargin barin wuta da wani jirginta ya yi kan farar hula a jihar Yobe.
Air Commodore Edward Gabkwet, mai magana da yawun NAF, ya bayyana a cikin wata sanarwa da aka aikewa Legit.ng.
Wani ɓangare na jawabin na cewa:
“Bayan bayanan sirri kan ayyukan Boko Haram / ISWAP a kan hanyar Kamadougou Yobe, an tura wani jirgin sama daga rundunar Sojin sama na Operation Hadin Kai don mayar da martani kan ayyukan ‘yan ta’addan da ake zargi a yankin da ke kan iyakar Najeriya/Nijar da misalin karfe 0600hrs a ranar 15 ga Satumba 2021.
"A yayin da jirgin yake aiki a Kudancin Kanama sai ya gano wani shige da fice da bai yarda da shi ba da yake da alaka da ayyukan 'yan ta'addan Boko Haram a duk sanda jirgin ke shawagi. Daga nan sai matukin jirgin ya bude wuta.
“Yana da mahimmanci a gane cewa yankin ya shahara kan ci gaban ayyukan Boko Haram/ISWAP. Abin takaici, rahotannin da suka iso hedkwatar NAF sun yi zargin cewa an kashe wasu fararen hula bisa kuskure yayin da wasu suka jikkata.
“Rahoton farko da ya karyata hatsarin ya ta'allaka ne a kan bayanan farko da rundunar sojin saman ta samu, wanda ke cewa jirgin yakin ya jefa bama-bamai ne a kan fararen hula.yayin da jirgin da aka tura don aikin ba ya dauke da bama -bamai.
"Saboda haka an kafa kwamitin bincike da zai yi cikakken bincike kan abin da ya faru."
Barin wuta ta sama: Gwamnan Yobe ya umurci asibitocin gwamnati da su kula da wadanda suka jikkata
A wani labarin, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala-Buni, ya umarci asibitocin gwamnati da ke Geidam da Damaturu da su bayar da magunguna kyauta ga waɗanda suka samu raunuka a lokacin farmakin jirgin yaki a ƙauyen Buhari da ke ƙaramar hukumar Yunusari ta jihar.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Daraktan yada labarai na jihar, Alhaji Mamman Mohammed ya fitar a ranar Alhamis, 16 ga watan Satumba.
Mala-Buni ya kuma umarci Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar da ta samar da kayan agaji don biyan bukatun gaggawa na iyalan mamatan da sauran mutanen gari, jaridar Punch ta ruwaito.
Asali: Legit.ng