Gwamnatin Buhari ta gargadi Yarbawa kan hada kai da kungiyoyin ta'addanci

Gwamnatin Buhari ta gargadi Yarbawa kan hada kai da kungiyoyin ta'addanci

  • Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa, ta yi mamakin yadda Yarbawa ke hada kai da kungiyar IPOB
  • A cewar fadar shugaban kasa, kungiyar IPOB kungiyar ta'addanci ne mai karfin soja 50,000
  • Wannan na zuwa ne bayan kungiyar Yarbawa ta hada kai da IPOB wajen gudanar da wata zanga-zanga a Amurka

Abuja - Fadar Shugaban kasa a ranar Laraba ta gargadi masu tayar da kayar baya 'yan awaren Yarbawa kan kawance da kungiyar ta'addanci mai fafutukar kasar Biyafra ta IPOB, The Nation ta ruwaito.

Ta bayyana tsoron cewa, alakarsu da IPOB ta sanya alamar tambaya a kan ikirarin su masu rajin kare hakkin Yarbawa ne.

Fadar Shugaban kasa ta nemi Majalisar Dinkin Duniya da ta yi watsi da bukatun da masu tayar da kayar bayan na Yarbawa, membobin IPOB a cikin Kasashen waje da sauran masu kunna rikici kasancewarsu masu rashin daidai da kimar kungiyoyin duniya.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Hotuna sun bayyana yayin da Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinonin INEC

Gwamnatin Buhari ta gargadi Yarbawa kan hada kai da kungiyoyin ta'addanci
Garba Shehu, Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Twitter

Hakanan a ranar Laraba 15 ga watan Satumba, Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila ya yi fatali da masu tayar da kayar baya, yana mai cewa babu banbanci tsakaninsu da kungiyar ISWAP da 'yan Boko Haram.

Jaridar The Sun ta ruwaito wani yankin sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar yana bayyana cewa:

"Abin mamaki ne, ganin yadda masu fafutukar "Yarbawa" a jiya (Talata) suka jefa kansu cikin 'yan asalin Biyafra (IPOB).
“IPOB kungiya ce da aka ayyana a matsayin ta ta’addanci. Yanzu ya bayyana a bainar jama'a kungiya na karfin soja 50,000."

'Yan aware sun yi zanga-zanga a kasar waje don nuna kin jinin kashe-kashe a Najeriya

Masu tayar da kayar baya na Kungiyar Yarbawa, tare da hadin gwiwar ‘yan kungiyar IPOB a kasashen waje a ranar Talata, sun gudanar da zanga-zanga a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York ta Amurka.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An hallaka Shugaban yan ta'addan ISWAP, AlBarnawy

A yayin zanga-zangar da kungiyar hadin kan 'yan asalin Najeriya ta NINAS ta shirya, masu tayar da kayar baya sun bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta sa ido kan zaben raba gardama a sassan Kudancin Najeriya da yankin Binuwai.

Sun kuma nemi a kawo karshen kashe-kashen da ake zargin makiyaya na aikatawa.

Ministan Buhari: Mu ilmantar da 'yan Najeriya ko kuma su addabi kasa da manyan kasa

A wani labarin, Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya ce hauhawar rashin aikin yi na kawo hadari ga Najeriya, Punch ta ruwaito.

Ya danganta rashin ilimi ga matsalolin da ke addabar kasar, yana mai gargadin cewa idan ba a yi maganin lamarin ba, kasar za ta iya “shafewa gaba daya.”

Ministan ya fadi haka ne a taron koli na tattalin arzikin hadin gwiwa da ma'aikatar ayyuka na musamman da harkokin gwamnatoci suka shirya a Abuja ranar Talata 14 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

Asali: Legit.ng

Online view pixel