Dan Majalisar Tarayya Ya Rigamu Gidan Gaskiya, Majalisa Ta Tafi Hutu Saboda Jimami

Dan Majalisar Tarayya Ya Rigamu Gidan Gaskiya, Majalisa Ta Tafi Hutu Saboda Jimami

  • Daga dawowa hutu, majalisar wakilai ta sake ɗage zamanta saboda mutuwar mambanta daga jihar Ondo, Adedayo Omolafe
  • Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, shine ya sanar da haka yayin zaman majalisar na yau Talata
  • Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi, ya bayyana gaban kwamitin tsaro na majalisar domin bayani kan harin NDA

Abuja - Majalisar wakilan tarayyar Najeriya ta sanar da ɗage zamanta zuwa 15 ga watan Satumba, 2021, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Majalisar ta dauki wannan matakin ne biyo bayan mutuwar ɗaya daga cikin mambobinta, Adedayo Omolafe.

Kafin mutuwarsa, Omolafe, shine yake wakiltar mazaɓun Akure ta kudu da Akure ta arewa, jihar Ondo, a majalisar wakilan Najeriya.

Yan majalisar tarayya sun sake tafiya hutu
Dan Majalisar Tarayya Ya Rigamu Gidan Gaskiya, Majalisa Ta Tafi Hutu Saboda Jimami Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, yayin da yake sanar da mutuwar Omolafe a zaman majalisar na Talata, yace majalisar ta saba ɗage zamanta matukar wani mambanta ya mutu.

Kara karanta wannan

Tsohon Dan Majalisar Dokoki da Wasu Mambobin Jam'iyyar Adawa Sun Sauya Sheka Zuwa APC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma kara da cewa shirye-shiryen jana'izarsa sun yi nisa kuma iyalansa zasu sanar da ranar gudanar da jana'izar.

Yaushe ɗan majalisar ya kwanta dama?

Omolafe, wanda aka fi sani da sunan "Mai Tsada" kuma mamba ne a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya mutu ne ranar 15 ga watan Agusta.

Legit.ng Hausa ta gano cewa majalisar ta dawo daga hutun da ta tafi tun ranar 26 ga watan Yuli ne yau Talata 14 ga watan Satumba.

Ministan tsaro ya bayyana gaban majalisa

Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya, ya bayyana gaban kwamitin tsaro na majalisar domin bayani kan harin da aka kai makarantar horar da jami'an sojoji NDA.

Kafin haka, kwamandan NDA, Manjo Janar Ibrahim Yusuf, ya ziyarci kwamitin domin yi wa yan majalisa bayani kan yadda aka samu matsalar tsaro a makarantar, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa ya gangara da motoci, ya hallaka mutane da yawa a Abuja

Kwamitin ya shiga ganawar sirri da ministan, a wani mataki da ya bayyana da cewa zata karɓi bayanan sirri na musamman.

A wani labarin kuma kungiyar malaman jami'o'i ASUU tace gwamnatin tarayya ce ke tilasta mata sake tsunduma yajin aiki

Kungiyar tace rashin aiwatar da sabon tsarin biyan albashi na UTAS, rashin sakin kuɗin alawus na EAA, da sauransu da FG ta yi ka iya tilastawa malaman sake shiga yajin aiki.

ASUU ta yi kira ga yan Najeriya kada su zargi kowa sai gwamnatin tarayya idan ƙungiyar ta sake rufe makarantu, kamar yadda leadership ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel