'Yan IPOB sun tare motar burodi sun sace dukkan abin da ke ciki, sun ƙona motar
- Wasu bata gari da ake zargin 'yan IPOB ne sun kaiwa motar jigilar burodi hari a Enugu
- Bata garin sun fizgo direban motar, suka sace dukkan abinda ke ciki sannan suka kona motar
- Daga bisani sojoji sun iso wurin sun tarwatsa bata garin ta hanyar harba bindiga a sama
Wasu mutane da ake zargin mambobin haramtaciyar kungiyar masu neman kafa kasar Biafara, IPOB, sun tare wata motar burodi a Enugu sun sace burodin sannan suka bankawa motar wuta a safiyar ranar Talata.
Lamarin ya faru ne a Emene, bayan garin babban birnin Enugu, a ranar da aka umurci mazauna garin su zauna a gida don nuna goyon baya ga Nnamdi Kanu, shugaban IPOB, Daily Trust ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani shaidan gani da ido ya ce an kona motar ne a tsohuwar kasuwar Orie Emene
Da ya ke bada labarin, shaidan ya ce:
"Direban shi ke da sanannen gidan burodi na Chimex a unguwar. Sun fito da direban da karfi da yaji, suka sace duka burodin sannan suka kona motar.
"Daga bisani sojoji sun iso wurin sun rika harbi a sama don tarwatsa bata garin. Babu wanda ya mutu. Ina kallon dukkan abin da ke faruwa daga nesa."
Daily Trust ta tattaro cewa wadanda ake zargin sun kuma sake kona wata motar da babur din adaidaita sahu.
Bata garin sun kai wa direban motan hayar hari sannan suka kona motar bayan korar fasinjojin.
An kona motar, kirar Sienna ne a mahadar Ibeagwa da ke layin Enugu-Opi a karamar hukumar Enugu ta Gabas.
Kazalika, an lalata wasu adaidaita sahu biyu a yankin.
An kona daya ne a mahadar PRODA, Emene yayin da dayan kuma aka kona shi dab da Jami'ar Coal City.
A lokacin hada wannan rahoton, hankulan mutane sun tashi a Emene, wajen babban birnin jihar Enugu.
Orji Kalu ga FG: Ku yafe wa magoya bayan Igboho da ke hannun ku kamar yadda kuka yafe wa ƴan Boko Haram
A wani labarin daban, bulaliyar majalisar dattawa, Sanata Orji Kalu ya bukaci gwamnatin tarayya ta yafe wa masu rajin kafa kasar Yarabawa, IPOB da ke hannun jami’an tsaro, The Cable ta ruwaito.
Tsohon gwamnan Jihar Abia ya ce ya kamata a yafe musu kamar yadda aka yafe wa tubabbun ‘yan Boko Haram da sauran ‘yan bindiga.
A wata takarda ta ranar Talata, 14 ga watan Satumba, Kalu ya ce yafe musu zai kawo hadin kai da zaman lafiya a kasar nan.
Asali: Legit.ng