Orji Kalu ga FG: Ku yafe wa magoya bayan Igboho da ke hannun ku kamar yadda kuka yafe wa ƴan Boko Haram

Orji Kalu ga FG: Ku yafe wa magoya bayan Igboho da ke hannun ku kamar yadda kuka yafe wa ƴan Boko Haram

  • Orji Kalu, bulaliyar majalisar dattawa, ya ce ya kamata a yafe wa masu rajin kafa kasar Yarabawa, IPOB dake hannun hukuma
  • Tsohon gwamnan jihar Abia ya ce ya kamata a yafe musu kamar yadda aka yafe wa tubabbun ‘yan Boko Haram da sauran ‘yan ta’adda
  • Kalu ya gabatar da wannan bukatar ta sa ne ta wata takarda a ranar Talata inda ya ce ayi hakan don samar da hadin kai a kasar nan

FCT Abuja - Bulaliyar majalisar dattawa, Sanata Orji Kalu ya bukaci gwamnatin tarayya ta yafe wa masu rajin kafa kasar Yarabawa, IPOB da ke hannun jami’an tsaro, The Cable ta ruwaito.

Tsohon gwamnan Jihar Abia ya ce ya kamata a yafe musu kamar yadda aka yafe wa tubabbun ‘yan Boko Haram da sauran ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

Kai Ɗan Kanzagi Ne, Muƙunshin Gishiri Ka Fi Gishiri Zaƙi, Gumi Ya Yi Wa Kakakin Buhari Wankin Babban Bargo

Orji Kalu ga FG: Ku yafe wa magoya bayan Igboho da ke hannun ku kamar yadda kuka yafe wa ƴan Boko Haram
Sanata Orji Uzo Kalu: Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalu ya ce yafiyar za ta kawo hadin kai a kasa

A wata takarda ta ranar Talata, 14 ga watan Satumba, Kalu ya ce yafe musu zai kawo hadin kai da zaman lafiya a kasar nan.

Kamar yadda The Cable ta ruwaito, Kalu ya ce:

“Na roki manyan kasar nan na arewa da kudu maso yamma su sanya baki don ba za mu iya ci gaba da zubar da jini ba”.
“Ina ci gaba da rokon su sannan gwamnatin tarayya ta amince don a samu zaman lafiya a kasar nan. An yafe wa ‘yan bindiga da sauran ‘yan ta’adda da dama don haka me zai hana a yafe musu."

Kalu ya ce:

“Na yarda da hadin kai a kasar nan, kuma na yarda da cewa kasar nan zata samu ci gaba matsawar akwai hadin mai, don haka ya kamata mu nemi hadin kan IPOB da mabiyan Sunday Igboho ta hanyar yafe musu".

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Afghanistan ya nemi afuwar mutanen ƙasar kan tserewar da ya yi Dubai ya bar su hannun Taliban

“Akwai bukatar a nemi hadin kan kowa a kasar nan. Haka manya suke yi, su bai wa gwamnatin tarayya shawara mai kyau don a samu zaman lafiya a kasar mu."

Sheikh Gumi ya faɗawa Fulani yadda za su yi wa kansu gata a Nigeria

A wani labarin daban, Malamin addinin musulunci mazaunin Kaduna, Dr Ahmad Gumi, ya yi kira ga fulani a su tabbatar sun yi rajista sun kuma karbi katin zabe gabanin babban zaben 2023 da ke tafe a kasar, Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa, samun katin zaben yana da muhimmanci domin hakan zai basu damar zaben shugabanni da za su yi jagoranci na gari sannan su kare musu hakkokinsu.

Gumi ya ce akwai bukatar Fulani su yi rajistan kamar sauran yan Nigeria, domin su zabi mutanen da za su kiyayye musu dabobinsu da dukiyoyinsu da rayukansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel