Yanzu-yanzu: Buhari ya aike wa majalisa sabuwar bukatar ranto $4bn, €710m
- Shugaba Muhammadu Buhari ya sake mika sabuwar bukatar ta rancen kudi har $4bn da €710m a gaban majalisar dattawan Najeriya
- Kamar yadda shugaban majalisar, Ahmad Lawan ya karanto wa majalisar, za a yi amfani da kudin wurin manyan ayyuka a bangarori daban-daban
- Wasikar ta bayyana cewa, manyan wurare kamar su bankin duniya, cibiyar habaka ta Faransa, bankin Exim da IFAD za su dauka nauyin bashin
Majalisar dattawa, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattawa da ta amince da sabuwar bukatarsa ta aron kudi har $4 biliyan da €710 miliyan.
Wannan na kunshe ne a wata wasika da aka mika da sunan shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, kuma aka karanta a zauren majalisar a ranar Talata, Daily Trust ta ruwaito.
Buhari ya ce wannan bashin da ake nema za a same su ta hannun masu mulki daga bankin duniya, cibiyar habaka ta Faransa, bankin Exim da IFAD.
Ya ce wannan bashin zai bai wa gwamnatin tarayya damar yin ayyuka masu matukar muhimmanci na jin dadin rayuwa a bangarori masu yawa, Daily Trust ta wallafa.
Wasikar ta ce:
"Na rubuto wannan wasika saboda abinda ku ka gani a sama kuma a hade da ita akwai karin kan shirin ranto kudi na 2018-2020 domin a duba kuma majalisa ta amince da su kafin su zama masu karbuwa.
"Shugaban majalisar dattawa zai iya tuna cewa mun kawo bukatar aron kudi na 2018-2020 domin majalisar dattawan ta amince da shi a watan Mayun 2021.
“Amma kuma, domin tabbatar da cewa dukkan abubuwan da ke tasowa kuma manyan ayyukan da FEC ta amince da su a watan Yunin da ya gabata sun tabbata, na sake turo kari kan wannan bukatar rancen.
“Ayyukan da aka lissafo za a yi daga rancen ana sa ran manyan wurare kamar bankin duniya, cibiyar cigaban Faransa, bankin EXIM da IFAD za su dauka nauyi inda za su bada $4,054,476,863 da €710 kuma jimilla ya kama $125 miliyan."
Ba zan lamunci uzirin kowa ba, COAS ya sanar da kwamandojin dakarun soji
A wani labari na daban, Shugaban dakarun sojin kasa, COAS Faruk Yahaya ya ja kunnen cewa ba zai lamunci uziri daga kwamandojin da ke jagorantar dakarun soji ba a filin daga da kuma yakar matsalar tsaron da kasar nan ke fuskanta ba.
Yahaya ya bada wannan wannan jan kunnen a yayin bude wani taro kashi na biyu da na uku na sojin da da ake hade a ranar Litinin a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.
Ya ce rundunar da ke karkashinsa za ta cigaba da mayar da hankali tare da kokarin ganin ana samun cigaba wurin yakar matsalolin da ake ciki.
Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan yari, sun saki fursunoni 240 sannan suka kashe sojoji a Kogi
Asali: Legit.ng