Gwamnatin Tarayya Ce ke Tilasta Mana Tsunduma Sabon Yajin Aiki, ASUU Ta Sake Magana

Gwamnatin Tarayya Ce ke Tilasta Mana Tsunduma Sabon Yajin Aiki, ASUU Ta Sake Magana

  • Ƙungiyar malaman jami'o'i ta kasa, ASUU, ta bayyana cewa yadda gwamnati ke jan kafa wajen cika alkawari ka iya jawo wani sabon yajin aiki
  • Kungiyar tace watanni 9 kenan da suka shuɗe bayan janye yajin aiki, amma gwamnati ta gaza cika alkawarinta
  • ASUU ta yi kira ga yan Najeriya kada su zargi kowa sai gwamnatin tarayya idan ƙungiyar ta sake rufe makarantu

Abuja - Ƙungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU), sashin Abuja, ta zargi gwamnatin tarayya da kokarin tilasta mata sake shiga wani sabon yajin aiki a faɗin ƙasa, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kungiyar tace rashin aiwatar da sabon tsarin biyan albashi na UTAS, rashin sakin kuɗin alawus na EAA, da sauransu da FG ta yi ka iya tilastawa malaman sake shiga yajin aiki.

Kara karanta wannan

Faɗawa Shugaba Gaskiya Yanzun Ya Zama Sabon Matsalar Tsaro a Najeriya, Malamin Addini Ya Magantu

ASUU tace ba zata tabbatar da cewa ba zata sake shiga sabon yajin aiki ba nan gaba duba da yadda gwamnati ta ɗauki aiwatar da yarjejeniyar MoA da aka cimma a baya.

ASUU ta sake barazanar shiga sabon yajin aiki
Gwamnatin Tarayya Ce Take Tilasta Mana Mu Tsunduma Sabon Yajin Aiki, ASUU Ta Sake Magana Hoto: withinnigeria.com
Asali: UGC

Shugaban ASUU reshen ɓangaren Abuja, Dakta Salahu Muhammed Lawal, shine ya bayyana haka a wurin taron manema labarai a Abuja, ranar Talata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shin laifin waye idan ASUU ta sake shiga yajin aiki?

Dakta Lawal ya yi kira ga yan Najeriya da kuma iyayen da ƴaƴansu ke karatu a jami'o'in gwamnati da kada su zargi kowa sai FG kan sakamakon da ka iya biyo baya idan ba'a aiwatar da MoA ba.

Yace:

"Idan baku manta ba kungiyar mu ta rattaɓa hannu kan yarjejeniyar MoA tare da gwamnati, wanda ya sa muka janye yajin aiki a watan Fabrairu, 2021."
"Amma watanni 9 sun shuɗe babu wani labari, ASUU na kira ga gwamnatin tarayya ta cika alkawarin da ta ɗauka, ta aiwatar da tsarin biyan albashi na malaman jami'o'i UTAS."

Kara karanta wannan

Ba zan sake soyayya ba, cewar dan sadan da budurwa ta yaudara bayan ya kashe mata kudin makaranta

FG ta saba mana haka - ASUU

Bugu da kari, Dakta Lawal yace gwamnati ta saba yiwa ƙungiyar haka, taki cika alƙawarin da ta ɗauka, matakin dake jawo sake tsunduma wani sabon yajin aiki.

Saboda haka, muna bukatar gwamnatin tarayya ta gaggauta aiwatar da daftarin yarjejeniyar MoA da aka cimma tsakanin ɓangarorin biyu ranar 7 ga watan Fabrairu.

A wani labarin kuma Tsohon Dan Majalisar Dokokin Jihar Yobe da Wasu Mambobin Jam'iyyar Adawa Sun Sauya Sheka Zuwa APC

Hukumar dillancin labarai ta Najeriya, (NAN), ta rahoto cewa a baya Babale ya wakilci mazaɓar Goya/Ngeji dake karamar hukumar Fika, a majalisar dokokin jiha.

Mataimakin gwamnan Yobe, Idi Gubana, ya tabbatar musu da cewa za'a tafi da su ba tare da nuna wani banbanci ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel