Ba zan sake soyayya ba, cewar dan sadan da budurwa ta yaudara bayan ya kashe mata kudin makaranta

Ba zan sake soyayya ba, cewar dan sadan da budurwa ta yaudara bayan ya kashe mata kudin makaranta

  • Wani jami'in dan sandan Kenya ya koka kan yadda wata budurwa ta ci amanarsa bayan ya kashe makudan kudade wajen taimaka mata tayi karatu
  • Sajen Moses Kimenchu ya ba da KSh 65,000 (N243,380) don taimaka mata shiga kwalejin horar da malamai, tare da fatan aurenta
  • Jami'in ya bayyana cewa a ƙarshe ta kashe wayarta kuma aka nemeta aka rasa a lokacin da za a kai gaisuwar iyaye

Kenya - Wani jami'in dan sandan Kenya ya magantu kan yadda ya dauki dawainiyar makarantar budurwar da yake so, kawai sai ga shi ta ci amanarsa.

A wata hira da gidan talabijin na TV47, Sajan Moses Kimenchu, wanda aka fi sani da Sergeant Saviour, ya ce lamarin ya faru ne bayan ya samu karin albashi a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Mwai Kibaki.

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

Ba zan sake soyayya ba, cewar dan sadan da budurwa ta yaudara bayan ya kashe mata kudin makaranta
Ba zan sake soyayya ba, cewar dan sadan da budurwa ta yaudara bayan ya kashe mata kudin makaranta Hoto: TV 47.
Asali: Facebook

Da yake ba da labarin abin da ya faru, Kimenchu ya ce yana da kuɗin da zai adana amma kuma ya zaɓi ya biya kuɗin makarantarta yayin da ta lashe zuciyarsa.

Ya dauki soyayyarsu da matukar muhimmanci, har yana ta shirye-shiryen aurenta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Na dauki lamarinta da gaske. Har na yi shirin aurenta. Don haka sau da yawa na kan je gidansu,” in ji shi.

Biyan kuɗin kakaranta da siyan keke

Kimenchu ya bayyana cewa ya bayar da KSh 65,000 (N243,380) don ba ta damar cimma burinta na samun horo a bangaren koyarwa.

Ƙari ga haka, ya saya mata keke don saukaka mata tafiya zuwa makaranta.

Kimenchu ya ce a ranar 2 ga Janairun 2008, ya yi niyyar daukarta don ganawa da danginsa.

Ta bace bat

Sai dai kuma, bayan bikin Kirsimeti, sai ta bace ma ganinsa.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 10 da aure, ya gwabje matarsa mai tsohon ciki saboda abinci, ta sheka barzahu

“Alikuwa mteja (ba a iya isa gare ta ba) daga ranar 30 ga Disamba. A ranar da za ta hadu da iyayena, na je gidanta amma babu wanda ya san inda take. Don haka dole na mika wuya,” in ji Kimenchu.

Dan sandan da ke cikin bacin rai ya dauki keken da ya saya mata ya jefar da shi a wani kogi da ke kusa. Ya yi rantsuwa ba zai sake soyayya ba.

Saurayina da muka yi shekaru 4 tare ya yi wuf da ƙawata da suka haɗu cikin watanni 6, Budurwa

A wani labarin, cikin takaici da cizon yatsa wata budurwa ta garzaya dandalin sada zumunta na zamani inda ta bayyana yadda saurayin ta ya yaudare ta, rahoton LIB.

A cewar ta ya yanke shawarar auren wata daban wacce ya hadu da ita ta wurin budurwar sa cikin watanni 6 kamar yadda LIB ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan kudu maso gabas ya ce ya yi wuri da za a fara zancen shugabancin Ibo, ya ba da dalili

Budurwar ta ce sun kwashe shekaru hudu su na kwasar soyayya ashe duk yaudarar ta yake shirin yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng