Tsohon Dan Majalisar Dokoki da Wasu Mambobin Jam'iyyar Adawa Sun Sauya Sheka Zuwa APC

Tsohon Dan Majalisar Dokoki da Wasu Mambobin Jam'iyyar Adawa Sun Sauya Sheka Zuwa APC

  • Tsohon ɗan majalisar dokokin jihar Yobe, Audu Babale, tare da wasu ɗumbin magoya bayansa sun sauya sheka zuwa APC
  • Babale ya bayyana cewa sun ɗauki wannan matakin ne saboda kyakkyawan jagorancin gwamna Mai Mala Buni
  • Mataimakin gwamnan Yobe, Idi Gubana, ya tabbatar musu da cewa za'a tafi da su ba tare da nuna wani banbanci ba

Yobe - Tsohon ɗan majalisar dokokin jihar Yobe, Audu Babale, tare da ɗumbin magoya bayansa sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, kamar yadda punch ta ruwaito.

Hukumar dillancin labarai ta Najeriya, (NAN), ta rahoto cewa a baya Babale ya wakilci mazaɓar Goya/Ngeji dake karamar hukumar Fika, a majalisar dokokin jiha.

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni
Tsohon Dan Majalisar Dokoki da Wasu Mambobin Jam'iyyar Adawa Sun Sauya Sheka Zuwa APC Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

A wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na mataimakin gwamnan jihar Yobe, Hussaini Mai-Suleh, ya fitar, ya bayyana cewa mutanen sun sauya sheka zuwa APC ne saboda kyakkyawan jagorancin gwamna Mai Mala Buni.

Kara karanta wannan

Da Ɗuminsa: Mataimakin Gwamna Ya Raba Gari da Gwamna, Zai Fice Daga Jam'iyyar PDP

Me sanarwar ta ƙunsa?

A cikin sanarwar, Mai Saleh yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Waɗanda suka sauya shekar sun ɗauki wannan matakin ne saboda ingantaccen jagorancin gwamnan Yobe, Mai Mala Buni."
"Babale yace ya yanke hukuncin komawa APC ne saboda kyakkyawan tsarin shugabanci na gwamna Mai Mala Buni, shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC ta ƙasa."

Babu nuna banbanci a APC

Bugu da kari sanarwar ta rahoto mataimakin gwamnan Yobe, Idi Gubana, yana tabbatarwa sabbin mambobin APC cewa ba za'a nuna banbanci ba tsakanin 'yaƴan jam'iyya.

Mataimakin gwamnan ya yi fatan waɗanda suka sauya shekan zasu bada gudummuwarsu wajen ciyar da APC gaba, kamar yadda dailynigerian ta ruwaito.

Gubana ya kara da cewa gwamna Buni a shirye yake ya tafi da kowa a gwamnatinsa, ba tare da duba bambancin siyasa ba.

Bani da shirin tsayawa takara a 2023 - Kakakin majalisa

Kara karanta wannan

Bayan Kwana 100 da Hana Hawa Twitter, Rahoto Ya Bayyana Biliyoyin Nairorin da Najeriya Ta Yi Asara

A wani labarin kuma Kakakin majalisar wakilan tarayya , Femi Gbajabiamila, ya yi watsi da jitar-jitar cewa zai tsaya takara a babban zaɓen 2023 dake tafe.

Kakakin majalisar ya bayyana cewa a halin yanzun ba shi da burin da ya wuce maida hankali sosai kan aikinsa na shugaban majalisar wakilai.

Gbajabiamila ya bayyana cewa yana son kafa tarihin da zai jima a zukatan yan Najeriya domin tunawa da gudummuwarsa wajen kawo cigaba a kasa lokacin mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel