Sabuwar doka: Gwamnatin jihar Jigawa ta sanya dokar hana babur a fadin jihar

Sabuwar doka: Gwamnatin jihar Jigawa ta sanya dokar hana babur a fadin jihar

  • Jihar Jigawa ta sanya sabuwar doka ta hana hawa babura a fadin jihar domin magance rashin tsaro
  • Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin jihar ta zauna zaman tattaunawa da kwamiin tsaron jihar
  • An bukaci 'yan jihar su bi wannar doka, sannan su tabbatar sun ba jami'an tsaro hadin kai wajen tabbatar da dokar

Jigawa - Gwamnatin Jigawa ta sanar da sanya dokar hana amfani da babura daga karfe 9 na dare zuwa karfe shida na safe a fadin jihar da nufin dakile karuwar rashin tsaro a sassan jihar, Channels Tv ta ruwaito.

Shugaban karamar hukumar Dutse kuma shugaban ALGON a jihar, Alhaji Bala Usman Chamo, ya bayyana cewa an yanke wannan shawarar ne a taron majalisar tsaro na jihar wanda Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar ya jagoranta.

Kara karanta wannan

Mataimakin Dirakta a ma'aikatar gwamnati ya hallaka kansa ranar da EFCC ta gayyaceshi

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin jihar Jigawa ta sanya dokar hana babur a fadin jihar
Taswirar jihar Jigawa | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Tribune Nigeria ta ruwaito cewa, Alhaji Bala Usman ya bayyana cewa "wannan wani bangare ne na matakan duba ayyukan masu aikata laifuka."

A cewarsa:

"Haramcin wani bangare ne a kokarin gwamnati na dakile 'yan ta'adda, ta amfani da babura wajen aikata laifuka, musamman a yankunan karkara na jihar."

Dalilan da suka jawo sanya dokar

Ya bayyana cewa an dauki matakin ne bayan Kwamitin Tsaro na jihar ya lura da karuwar barazanar tsaro a jihar.

Shugaban ALGON ya ci gaba da cewa:

“An lura cewa tsaro yana kara tabarbarewa a cikin kasar da jihar a matakin karamar hukumar mu. Mun samu faruwar matsalolin tsaro da dama a fadin jihar.
"Kuma wannan shine abin da ya haifar da shawarar kwamitin tsaro na sanya wasu matakai don sarrafa duk wani abin da zai iya haifar da karuwar matsalolin tsaro.

Kara karanta wannan

Kisan Jos: Na kudiri aniyar gurfanar da 'yan ta'adda a gaban kuliya, inji Buhari

“Kuma matakin da aka dauka shi ne hana amfani da yawon babura daga karfe 9 na dare zuwa karfe 6 na safe, har sai an kara fitar da wata sanarwa. Duk wannan ya shafi dukkan kananan hukumomi 27 na jihar."

An sanar da wadanda abin ya shafa

Shugaban ya kara da cewa an sanar da jagororin 'yan achaba game da ci gaban don isarwa ga membobin su.

Ya kara da cewa, an kuma aika da sako ga dukkan hukumomin tsaro don tabbatar da aiwatar da umarnin kamar yadda kwamitin tsaro ya bayar da umarni.

Usman ya kara da cewa:

"Yana da mahimmanci a lura cewa duk wanda aka samu ya saba wa umarnin za a yi hukunta shi
"Duk da haka, za a kebe wasu inda aka samu dalili mai ma'ana."

Tsaro: Gwamnati ta ba da umarnin a katse sabis din layukan waya a Zamfara

A wani labarin, Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta umarci dukkan kamfanonin sadarwa da su katse hanyoyin sadarwarsu a jihar Zamfara, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Barazanar tsaro: Jihar Adamawa ta rufe makarantu 30 na kwana saboda rashin tsaro

A daya daga cikin wasikun da aka aike wa kamfanonin, mataimakin shugaban hukumar Umar Danbatta a ranar Juma'a 3 ga watan Satumba ya ce matakin na daya daga cikin dabarun da jami'an tsaro ke bi na dakile 'yan bindiga da ke addabar jihar.

A cewarsa:

“Matsalar tsaro a jihar Zamfara ta sanya dole a kkatse dukkan ayyukan sadarwa a jihar daga yau 03 ga Satumba, 2021."

Asali: Legit.ng

Online view pixel