Mataimakin Dirakta a ma'aikatar gwamnati ya hallaka kansa ranar da EFCC ta gayyaceshi
- Ana zargin babban jami'in gwamnati da daukan ran kansa ranar da ya kamata ya bayyana gaban EFCC
- Hukumar da yake yiwa aiki tace ba za ta cewa komai kan lamarin ba
- Wannan abu ya faru ne a unguwar Lugbe ta birnin tarayya Abuja
Abuja - Mataimakin dirakta a hukumar cigaban fasahar ilmin halitta watau National Biotechnology Development Agency (NABDA), Mr Christopher Orji, da alamun ya halaka kansa a Abuja.
An tsinci gawar Orji ne rataye kan fanka a gidansa dake Federal Housing Authority Estate, Lugbe, Abuja, misalin karfe 4 na yammacin ranar 30 ga Agusta, 2021.
Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar yan sanda har yanzu na kan gudanar da bincike kan lamarin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Orji ya mutu yana mai shekaru 59.
Rahotanni sun nuna cewa hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta gayyacesa zuwa ofishinta dake Abuja ranar da ya mutu.
Amma wani ma'aikacin hukumar wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace ba zai yiwu ace Orji ne ya kashe kansa ba saboda ba'a samu wani wasika na wasiyya ba a gidansa.
Yayinda aka tuntubi jami'in hulda da jama'a na NABDA, Nkiru Amakeze, yace bashi da ta cewa kan lamarin.
Asali: Legit.ng