Barazanar tsaro: Jihar Adamawa ta rufe makarantu 30 na kwana saboda rashin tsaro

Barazanar tsaro: Jihar Adamawa ta rufe makarantu 30 na kwana saboda rashin tsaro

  • Jihar Adamawa ta rufe wasu makarantun sakandare saboda ta'azzarar lamurran tsaro a kasar
  • Gwamnatin jihar ta bayyana haka ne ta bakin kwamishinan ilimi na jihar ta Adamawa a fadar jihar
  • Gwamnati ta kuma bayyana cewa, hakan wani yunkuri ne na kare dalibai daga fadawa hadarin 'yan bindiga

Adamawa - Gwamnatin jihar Adamawa ta sanar da rufe makarantun sakandire na kwana 30 da ke jihar daga cikin kananan makarantu 34 saboda matsalar rashin tsaro.

Rufewar, a cewar wata sanarwa daga kwamishiniyar ilimi , Mrs. Wilbina Jackson, za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Satumba, 2021 har sai an sake samun wani ci gaba.

Sanarwar da wakilin jaridar Punch ta gani ta ce daukar wannan mataki wani yunkuri ne na tabbatar da tsaron dalibai saboda rashin tsaro da ke addabar kasar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi ya aurar da diyarsa Hauwa ga dan Sarkin Azara

Da dumi-dumi: Jihar Adamawa ta rufe makarantu 30 na kwana saboda rashin tsaro
Taswirar jihar Adamawa | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Matakin na gwamnatin jihar ya zo ne a yayin da ake ci gaba da samun karuwar ‘yan bindiga a kasar, lamarin da ya yi sanadiyar sace daruruwan yara 'yan makaranta a jihohi da dama.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Makarantu hudu da rufewar ba za ta shafa ba sune Makarantar Sakandaren 'Yan Mata ta Gwamnati dake Yola; Kwalejin Janar Murtala Mohammed ta Yola; Makarantar Jada ta Musamman; da Makarantar Mubi ta Musamman.

Wani yankin sanarwar ya kara da cewa:

“Wannan ya zama dole saboda kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta a yanzu da kuma duba da karancin shekarun dalibai, saboda haka ake bukatar su yi karatu karkashin kulawar iyayensu.
”Za a sanya dukkan daliban makarantun da abin ya shafa a makarantun sakandaren gwamnati mafi kusa da su a cikin wuraren da suke da zama. Masu ruwa da tsaki, PTA, ANCOPS da sauran su za su tabbatar da bin wannan manufar ta gwamnati."

Kara karanta wannan

Tsaro: Gwamnati ta ba da umarnin a katse sabis din layukan waya a Zamfara

Gwamnati ta ba da umarnin a katse sabis din layukan waya a Zamfara

A Zamfara kuwa, Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta umarci dukkan kamfanonin sadarwa da su katse hanyoyin sadarwarsu a jihar Zamfara, Daily Nigerian ta ruwaito.

A daya daga cikin wasikun da aka aike wa kamfanonin, mataimakin shugaban hukumar Umar Danbatta a ranar Juma'a 3 ga watan Satumba ya ce matakin na daya daga cikin dabarun da jami'an tsaro ke bi na dakile 'yan bindiga da ke addabar jihar.

A cewarsa:

“Matsalar tsaro a jihar Zamfara ta sanya dole a kkatse dukkan ayyukan sadarwa a jihar daga yau 03 ga Satumba, 2021.
"Wannan zai baiwa hukumomin tsaro da suka dace damar aiwatar da ayyukan da ake bukata don magance kalubalen tsaro a jihar, daidai da bukatun, an umarci Globacom da ta rufe dukkan shafuka a jihar Zamfara da kowane rukunin yanar gizo a cikin makwabciyar jihar da za ta iya bayar da sabis na sadarwa a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamnatin Kaduna ta haramta safarar dabbobi daga wasu jihohi

“Rufe shafin na sati biyu ne (03 ga Satumba - 17, 2021) a matakin farko. Ana bukatar daukar matakin gaggawa a wannan batun.”

Kisan gilla a Jos: Hukuma taci alwashin kame mazauna yankunan da ake kashe-kashe

A wani labarin, Hukumomin karamar hukumar Jos ta Arewa, a ranar Lahadin da ta gabata, sun ce za su bibiyi duk wani mutumin da ya kai hari kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba kuma su kama su don fuskantar fushin doka, Daily Trust ta ruwaito.

Sun kuma ce za su cafke mazauna unguwar ko yankin da abin ya faru don tabbatar da abin da ya dace idan wadanda ake zargi suka tsere.

Wannan ci gaban na zuwa ne bayan harin da aka kai wa matafiya musulmai a ranar 14 ga watan Agusta a kusa da hanyar Gada-biyu-Rukuba na karamar hukumar Jos ta Arewa da kuma tashin hankalin da ya biyo baya a wasu yankuna.

Kara karanta wannan

Atiku: Ya kamata a kirkiri rundunar 'yan sandan da aikinta shine gadin makarantu

Asali: Legit.ng

Online view pixel