'Yan Bindigan Zamfara Na Neman Fushin Allah Ya Sauka a Kansu, Sheikh Abdullahi Dalla-Dalla

'Yan Bindigan Zamfara Na Neman Fushin Allah Ya Sauka a Kansu, Sheikh Abdullahi Dalla-Dalla

  • Sheikh Abdullahi Dalla-Dalla, babban limamin masallacin Juma'a na Sambo Dan Asafa da ke Gusau ya gargadi 'yan bindigan jihar
  • Sheikh Dalla-Dalla yayin hudubarsa na ranar Juma'a ya shaidawa 'yan bindigan cewa fushin Allah zai sauka a kansu idan ba su tuba ba
  • Babban malamin ya yi gargadin cewa zubar da jinin mutane babban laifi ne kuma ya bukaci al'ummar jihar su cigaba da addu'a domin Allah ya magance musu matsalar

Babban limamin masallacin Juma'a na Sambo Dan-Ashafa da ke Gusau, Sheikh Abdullahi Dalla-Dalla, a ranar Juma'a ya gargadi 'yan bindigan da ke jihar su janye ko su gamu da fushin Allah, Daily Nigerian ta ruwaito.

A yayin hudumar Juma'a da ya yi, ya ce kashe mutane da keta hakkinsu a jihar zai haifar da fushin Allah, idan har masu aikata laifin ba su tuba sun dena ba kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi awon gaba da yayan Sakataren Gwamnatin jihar Katsina

'Yan Bindigan Zamfara Na Neman Fushin Allah Ya Sauka a Kansu, Sheikh Abdullahi Dalla-Dalla
Taswirar Jihar Zamfara. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Dalla-Dalla ya ce:

"Abin da na ke kira ga 'yan bindigan shine su tuba; su dena kashe mutanen da ba-su-ji-ba-ba su gani ba sannan su mika mukamansu kafin fushin Allah ya sauka a kansu.
"Wannan babban abun damuwa ne ga masu ruwa da tsaki. A matsayin mu na musulmi, mu cigaba da yin addu'o'i.
"Mu yi addu'ar ga Allah mu nemi taimakonsa game da kallubalen tsaro da ke kara tabarbarewa a jihar."

Jihar Zamfara na daga cikin jihohin da hare-haren yan bindigan ya tsananta.

Hakan ya shafi noma da kasuwanci saboda yadda yan bindigan ke zuwa su sace mutane a gonaki ko kai hari a ƙauyukan.

A shekarar 2019 gwamantin jihar Zamfara ta yi yarjejeniyar sulhu da yan bindigan.

Kara karanta wannan

Mu koma ga Allah: Matawalle ya buƙaci al'umma su yi addu'o'i game da ƴan bindiga

Sai dai duk da hakan har yanzu ana ci gaba da kai hare-haren kuma ana sace mutane ko halaka su.

'Yan bindiga sun afka ofishin ƴan sandan Zamfara, sunyi kisa, sun sace bindigu AK-47 masu yawa

A wani labarin daban, wasu ɓata gari da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun kai hari ofishin yan sanda a Zamfara sun kashe jami'in ɗan sanda ɗaya, rahoton SaharaReporters.

Yan bindiga sun kuma kashe wani shugaban ƴan banga da wasu mutane biyu a garuruwan Nahuce da Gidan Janbula a ƙaramar hukumar Bungudu.

Har wa yau, ƴan bindigan sun yi awon gaba da mutane hudu yayin da suka kawo harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel