Yan bindiga sun yi awon gaba da yayan Sakataren Gwamnatin jihar Katsina

Yan bindiga sun yi awon gaba da yayan Sakataren Gwamnatin jihar Katsina

  • Matsalar yan bindiga na cigaba da munana a jihar Katsina, mahaifar shugaban kasa
  • Duk da sabbin dokokin da gwamna Masari ya sanya, ana cigaba da sace mutane
  • Gwamna Masari ya kalubalanci hukumar yan sanda

Katsina: Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da Kabir Muhammad Burkai, yaya ga Sakataren gwamnatin Katsina, Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa.

Katsina Post ta ruwaito cewa yan bindigan sun saceshi ne ranar Laraba, 1 ga Satumba, 2021 a gonar sa dake wani kauye mai suna Daftau da rana, karamar hukumar DanMusa ta jihar.

Kabir Muhammad Burkai dai mahaifin su daya da Mustapha Inuwa sai dai ba mahaifiyar su daya ba.

Sai dai har ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, ba’a samu labarin ko an sako shi ba kuma ‘yan bindigar ba su tuntubi yan uwansa ba.

Kara karanta wannan

Yallabai ba kada isasshen jami'an da zasu iya samar da tsaro a Katsina, Masari ga IGP Alkali

Kabir Muhammad Burkai dai tsohon jami’in dan sanda ne da yayi ritaya kuma manomi ne.

Yana zaune ne da iyalan sa a garin Danmusa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan bindiga sun yi awon gaba da yayan Sakataren Gwamnatin jihar Katsina
Yan bindiga sun yi awon gaba da yayan Sakataren Gwamnatin jihar Katsina Hoto: Mustapha Inuwa
Asali: Facebook

Babu isassun yan sanda da zasu kare jihar Katsina

Gwaman jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya yi ikirari hukumar yan sanda ba tada isasshen jami'an da zasu samar da tsaro kan jiha mai adadin mutane milyan takwas.

Masari ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin Sifeto Janar na yan sanda, Alkali Usman Baba, a gidan gwamnatin jihar, ranar Alhamis, DailySun ta ruwaito.

Masari yace babu isassun yan sandan da zasu iya bada tsaro a jihar Kastina.

A cewarsa:

"Jihar Katsina na da mutane kimanin milyan takwas amma yan sanda nawa muke da shi a Katsina.?"
"A nawa lissafin na adadin yan sandan dake kananan hukumominmu, ban tunanin muna da yan sanda 3,000 a jihar."

Kara karanta wannan

Tubabbun 'yan bindiga sun koma ruwa, sun shiga hannun 'yan sanda a Katsina

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng