'Yan bindiga sun afka ofishin ƴan sandan Zamfara, sunyi kisa, sun sace bindigu AK-47 masu yawa

'Yan bindiga sun afka ofishin ƴan sandan Zamfara, sunyi kisa, sun sace bindigu AK-47 masu yawa

  • 'Yan bindiga sun kai hari ofishin rundunar yan sanda da ke Nahuce a jihar Zamfara
  • Yan bindigan sun halaka jami'in dan sanda daya sun kuma sace bindigu kirar AK-47 da dama
  • Har wa yau, yan bindigan sun kuma halaka wani shugaban yan banga sun kuma sace mutane guda hudu yayin harin

Wasu ɓata gari da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun kai hari ofishin yan sanda a Zamfara sun kashe jami'in ɗan sanda ɗaya, rahoton SaharaReporters.

Yan bindiga sun kuma kashe wani shugaban ƴan banga da wasu mutane biyu a garuruwan Nahuce da Gidan Janbula a ƙaramar hukumar Bungudu.

'Yan bindiga afka ofishin ƴan sandan Zamfara, sunyi kisa, sun sace bindigu AK-47 masu yawa
Taswirar Jihar Zamfara. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Har wa yau, ƴan bindigan sun yi awon gaba da mutane hudu yayin da suka kawo harin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun afka wa wani gari a Niger, sun sace kaya a shaguna da kuɗaɗen mutane

Yadda harin faru?

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Juma'a yayin da yan bindigan masu yawa dauke da muggan makamai suka kutsa Ofishin yan sanda a Nuhuce da ƙauyukan da ke kusa da shi.

Yan bindigan sun shafe fiye da awa ɗaya suna musayar wuta da yan sanda da yan banga kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

An ce sun tafi da wasu bindigu kirar AK-47 mallakar yan sandan.

Jihar Zamfara na daga cikin jihohin da hare-haren yan bindigan ya tsananta.

Hakan ya shafi noma da kasuwanci saboda yadda yan bindigan ke zuwa su sace mutane a gonaki ko kai hari a ƙauyukan.

A shekarar 2019 gwamantin jihar Zamfara ta yi yarjejeniyar sulhu da yan bindigan.

Sai dai duk da hakan har yanzu ana ci gaba da kai hare-haren kuma ana sace mutane ko halaka su.

Kashe-Kashen Jos: CAN ta miƙa muhimman saƙo ga shugabannin musulmi da kirista a Plateau

Kara karanta wannan

'Yan banga sun bindige mai garkuwa da mutane yayin da ya je karbar kudin fansa

A wani labarin daban, Kungiyar kirista ta Nigeria, CAN, a Jos, babban birnin jihar Plateau ta roki shugabannin musulmi da na kirista su dena tunzura mutane suna miyagun ayyuka, Peoples Gazette ta ruwaito.

A cewar sanarwar da ta fitar a garin Jos a ranar Laraba mai dauke da sa hannun shugaban CAN, Polycarp Gana da satare Ezekiel Noam, kungiyar ta kuma yi Allah wadai da kashe-kashen da aka yi a Yalwan Zangam.

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun afka garin a daren ranar Talata sun kashe mutane masu yawa sannan suka kona gidaje da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164