Mu koma ga Allah: Matawalle ya buƙaci al'umma su yi addu'o'i game da ƴan bindiga
- Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bukaci mutanen jiharsa su dage da roƙon Allah bisa harin ƴan bindiga
- Gwamna Matawalle ya bayyana hakan ne yayin da ya hallarci wata addu'a ta musamman a babban masallacin Gusau
- Matawalle ya ce addu'a ce takobin mumini ya kuma kamata mutanen jihar su taimakawa gwamnati da jami'an tsaro da addu'a
Gusau - Jihar Zamfara - Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya yi kira ga al'ummar jihar Zamfara su tsananta addu'o'i domin Allah ya kawo ƙarshen matsalar ƴan bindiga a jihar.
The Punch ta ruwaito cewa Matawalle ya yi wannan kirar ne yayin wani taron addu'a na musamman da kwamitin tuntuɓa ta Ulamau ta shirya a jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gwamnan wanda ya hallarci sallar Juma'a a babban masallacin Gusau ya ce ya zama dole al'umma su taimakawa gwamnati da jami'an tsaro wurin samar da tsaro a jihar, rahoton The Punch.
Addu'a ce takobin mumini, Matawalle
Ya ce:
"Addu'a shine babban makamin da zai iya maganin kowanne bala'i. Ya zama dole mu tuba ga Allah."
Kamfanin Dillancin Labari, NAN, ta ruwaito cewa an yi addu'o'in na musamman a dukkan masallatai Juma'a a Jihar.
Jihar Zamfara na daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren yan bindiga a arewa maso yammacin Nigeria.
A baya-bayan nan wasu yan bindigan sun afka wata makaranta a jihar Zamfara sun sace dalibai kamar yadda rundunar yan sandan jihar ta tabbatar.
'Yan sanda sun damke ma'aikacin banki da ya kwashewa kwastoma N10m daga asusunsa
A wani labarin daban, Hukumar ‘yan sandan jihar Oyo sun kama wani Adeyemi Tosin, mai shekaru 36, wanda ma’aikacin banki ne bisa zarginsa da kwasar naira miliyan 10 daga asusun wani abokin huldar bankin, Oladele Adida Quadri.
Kakakin hukumar, DSP Adewale Osifeso, ya bayyana hakan a wata takarda a ranar Talata, 17 ga watan Augusta, inda yace Tosin ya saci kudin Quadri, mai shekaru 78 ne da sunan zai taimake shi a reshen bankin na Ibadan bisa matsalar da ya samu wurin cirar kudi a ranar 12 zuwa ranar 13 ga watan Augusta.
Binciken ‘yan sandan ya haifi da mai ido sakamakon umarnin kwamishinan ‘yansandan jihar, Ngozi Onadeko, wacce tasa a yi bincike na musamman.
Asali: Legit.ng