Mata ta bukaci alkali ya tsinke igiyar auren su na shekaru 18 saboda mijinta ya ki yin riga-kafin COVID-19

Mata ta bukaci alkali ya tsinke igiyar auren su na shekaru 18 saboda mijinta ya ki yin riga-kafin COVID-19

  • Wata mata ta nemi a raba auren su mai shekaru 18 saboda mijin ta ya ki yarda a yi masa riga-kafin COVID-19
  • A cewarta, mijin ta ya na fama da ciwon numfashi kuma ya yi COVID-19 a 2020 suka hadu suka fara taba masa huhunsa
  • A dalilin haka ne yasa ta ce ba za ta iya ci gaba da rayuwa da wanda bai san ciwon kan sa ba balle ta sa rayuwarta a hatsari

South Africa - Wata mata ‘yar kasar Afirka ta kudu ta maka mijinta a kotu ta na bukatar a raba aurensu mai shekaru 18 bayan ya ki yarda a yi masa riga-kafin cutar COVID-19.

Ta bayyana yadda mijinta, Graham Spies ya yi fama da cutar COVID-19 a shekarar 2020. Charnelle ta sanar da News24 cewa ba ta kara bata lokaci ba ta yi gaggawar amsar allurar cutar.

Kara karanta wannan

Sace dalibai 73 a Zamfara: ACF ta dau zafi, ta ce duk gwamnatin da ba za ta kare al’umma ba bata da amfani

Mata ta bukaci alkali ya tsinke igiyar auren su na shekaru 18 saboda mijinta ya ki yin riga-kafin COVID-19
Mata ta bukaci alkali ya tsinke igiyar auren su na shekaru 18 saboda mijinta ya ki yin riga-kafin COVID-19. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

Ta ce idan har ba zai amshi riga-kafin ba, ba ta ga dalilin da zai sa ta cigaba da zama da shi ba, kuma hakan ya na nuna cewa bai iya kulawa da kan sa ba balle mutanen da suke kewaye da shi, LIB ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda Charnelle tace:

“Graham ya yi fama da cutar COVID-19 a shekarar da ta gabata kuma ina ganin yadda yayi ta fama kamar zai mutu, ba zan so in ga wani a irin wannan yanayin ba.
Cutar ta kama huhunsa sannan kuma ya na da ciwon asma wanda hakan ya ja numfashin sa ya sarke. Yadda na ga an sallamo shi a asibiti a shekarar da ta gabata, ya yi matukar ba ni mamaki don hakan ikon Ubangiji ne kawai.
“Ba zan taba iya sadaukar da lafiya ta ba. Shiyasa a shekarar da ta gabata na shaida wa Graham cewa matukar ya ki amsar riga-kafin, ba zan ci gaba da zama da shi ba. Saboda na lura ba zai iya kulawa da kansa ba balle mutanen da ke kewaye da shi.”

Kara karanta wannan

Shekaru 35 yana aikin koyarwa a Borno, dan Najeriyan da Turawa suka horar ya koma talla

A bangaren Graham, cewa ya yi bai amshi allurar riga-kafi ba ne kawai saboda ba shi da ra’ayi. A cewar sa;

“Na yarda da kimiyya a wani bangaren. Bana son a mayar da ni beran masar din da za a dinga yi wa allura. Babu tabaccin allurar ta na aiki dari bisa dari.”

A cewarsa, matarsa, ta bashi mamaki bayan tsawon shekarun da suka yi, duk fadace-fadacen da suka yi suka shirya kusan shekaru 20, sai allura ce za ta zama sanadiyyar rabuwar aurensu.

Graham ya kara da cewa;

“Ba haka na zaci karshen aure na zai zo ba. Tabbas mun samu matsaloli, amma babu wanda yake dari bisa dari. Amma wajibi ne kowa yayi abinda yake tunanin daidai ne.”

An daura auren su a Cape Town a shekarar 2003, sai dai har yanzu ba su samu da ko daya ba kuma sun sayar da komai nasu don su canja gari saboda ayyukan su.

Kara karanta wannan

Yajin-aiki: A zargi Gwamnatin Najeriya idan muka dauki mataki na gaba inji Kungiyar ASUU

Charnelle ta kara da cewa, babu dalilin da zai sa ta sa rayuwar yaran da bata haifa ba a hatsari.

"Mun dade muna yin maganar nan kuma na ce masa ba zan taba haihuwa da shi ba matsawar bai yi riga-kafi ba. Na yi matukar takaicin yadda miji na wanda na fi kauna ya ke kokarin gurgunta rayuwar yaranmu ta hanyar kin yin riga-kafi. Wannan hauka ne.

A ranar 22 ga watan Satumba ma’auratan za su sanya hannu a takardun rabuwar auren su.

Ka yi wa sojojin da suka yi bore afuwa kamar yadda ka yi wa tubabban ƴan ta'adda, Falana ga Buhari

A wani labari na daban, babban lauyan Nigeria mai rajin kare hakkin bil adama, Femi Falana (SAN), ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa sojoji 70 da aka samu da laifin bore afuwa, The Cable ta ruwaito.

An samu sojojin da laifin yi wa shugabanninsu bore a Maiduguri, Jihar Borno a shekarar 2014 kuma daga bisani aka yanke musu hukunci.

Kara karanta wannan

Idan babu namijin da ya furta maki so, ki yi amfani da asiri, wata budurwa ta bayar da shawara a bidiyo

Da farko an yanke wa sojojin hukuncin kisa amma a 2015, bayan Falana ya rika bibiyar shar'arsu, an sauya hukuncin zuwa daurin shekaru 10 a gidan gyaran hali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel