Yajin-aiki: A zargi Gwamnatin Najeriya idan muka dauki mataki na gaba inji Kungiyar ASUU

Yajin-aiki: A zargi Gwamnatin Najeriya idan muka dauki mataki na gaba inji Kungiyar ASUU

  • Kungiyar malaman jami’a za ta kira taron gaggawa na majalisar NEC
  • ASUU za ta yi wannan taro bayan wa’adin da ta ba gwamnati ya cika
  • Shugaban ASUU yace a zargi gwamnati a kan matakin da za su dauka

Abia - Kungiyar malaman jami’a na kasa, ASUU, ta fara maganar kiran taron gaggawa na majalisar koli ta NEC a makon nan, domin tayi zama.

Jaridar The Nation ta ce hakan ya zama dole ne bayan wa’adin da kungiyar ta ASUU ta ba gwamnatin tarayya ya cika a karshen watan Agusta.

Wani mataki ASUU za ta dauka a yanzu?

Bayan wannan zama, ASUU tace za ta tattauna da duk masu fada-a-ji a duka rassan kungiyar, idan dai gwamnati ta gaza cika alkawuran da ta dauka.

Gwamnatin tarayya ba ta ce uffan ba yayin da wa’adin da aka ba ta ya cika a ranar Talata. Jaridar ta nemi jin ta bakin Chris Ngige, amma ba ta dace ba.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa Malaman Jami’a ba za su fara yajin-aiki a yau ba inji Shugaban ASUU

Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana cewa a zaman NEC da za ayi, malaman za su san matsayar da za a dauka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Emmanuel Osodeke ya bayyana cewa ba shi da ikon da zai tashi rana-tsaka, yace za a fara yajin-aiki.

Shugaban Kungiyar ASUU
Minista da Sabon shugaban ASUU Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

“ASUU ba ta kawo maganar zuwa yajin-aiki, mun ce idan gwamnati ba ta biya mana bukatunmu zuwa Agusta ba, za mu zauna, mu san matakin da za a dauka.”
“Amma kasar nan ta kama gwamnatin tarayya da laifi a kan duk wata matsaya da muka dauka, abin da muka ce kenan, ba mu ambaci za a shiga yajin-aiki ba.”
“Shugaban ASUU ba zai iya farka wa rana guda kurum yace za a shiga yajin-aiki ba, ko shugabannin kungiyar sai sun tuntubi rassan sauran jami’o’i.”

Da yake magana a ranar Talata, Farfesa Osodeke yace a ranar ne wa’adin zai cika, don haka za a yi zaman NEC domin ‘yan kungiyar su san abin da za ayi.

Kara karanta wannan

Yajin-aiki: Yau Malaman Jami’a za su dauki matsaya inji Shugaban kungiyar ASUU

Sai NEC ta zauna

A jiya ne wa’adin da kungiyar ASUU ta ba gwamnatin ya cika, amma Dr. Dele Ashiru yace akwai wsu matakan da ake bi, kafin a dunguma da yajin-aiki a jami'o'i.

Dele Ashiru wanda shi ne shugaban ASUU na reshen UNILAG yace ba haka nan za a soma yajin-aiki ba, sai malaman jami'an sun yi taron majalisar NEC tukuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel