Sace dalibai 73 a Zamfara: ACF ta dau zafi, ta ce duk gwamnatin da ba za ta kare al’umma ba bata da amfani
- Kungiyar Arewa Consultative Forum ta yi Allah wadai da sace dalibai guda 73 da wasu 'yan bindiga suka yi a jihar Zamfara
- ACF ta bayyana cewa babu wani amfani a wanzuwar gwamnati da ba za ta iya kare al'ummanta ba
- A ranar Laraba, 1 ga watan Satumba ne dai 'yan bindigar suka kai farmaki wata makaranta da ke karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara sannan suka yi awon gaba da dalibai da dama
Kaduna - Kungiyoyin Arewa Consultative Forum, da Southern Kaduna Peoples Union sun yi Allah wadai da sace dalibai 76 da wasu ‘yan bindiga suka yi a jihar Zamfara a jiya Laraba, 1 ga watan Satumba.
Sakataren yada labarai na kungiyar ACF, Emmanuel Yawe, ya bayyana bakin cikinsa kan sabon harin da sace daliban.
Kakakin na ACF ya shaida wa jaridar Punch a Kaduna, a ranar Laraba, cewa kungiyar ta arewacin kasar ba ta jin dadin ayyukan 'yan fashi da ke gudana a yankin.
Duk gwamnatin da ba za ta iya kare 'yan kasa ba ba ta da amfani - ACF
Yawe ya bayyana cewa duk gwamnatin da ba za ta iya kare 'yan kasarta ba toh lallai ba ta da wani amfani na wanzuwa.
Ya ce:
"To, wani mataki Matawalle ya dauka? Bai kamata mutane su yi sanarwa ba kawai. Idan yana kira ga jama'a su tashi su kare kansu, ya kamata ya iya yin kari a duk kokarin da jama'a ke yi."
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai da dama a wata makaranta a jihar Zamfara
Idan babu namijin da ya furta maki so, ki yi amfani da asiri, wata budurwa ta bayar da shawara a bidiyo
Da farko mun kawo cewa wasu ‘yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai farmaki wata makaranta da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara.
An tattaro cewa maharan sun kuma yi awon gaba da wasu dalibai da dama a makarantar wacce take ta maza da mata a hade.
Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa mazauna garin Kayan Maradun sun sanar da ita cewa lamarin ya afku ne a safiyar ranar Laraba, 1 ga watan Satumba. Sun kuma bayyana cewa ba a san adadin daliban da maharan suka sace ba.
Hukumar yan sanda ta bayyana adadin daliban da aka sace a jihar Zamfara
Hakazalika hukumar yan sandan jihar Zamfara ta bayyana adadin daliban da aka sace a makarantar GDSS Kaya dake karamar hukumar Maradun ta jihar a ranar Laraba.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, Muhammadu Shehu, a jawabin da ya saki yace yara 73 yan bindigan suka dauke, TVC ta ruwaito.
Asali: Legit.ng