Shekaru 35 yana aikin koyarwa a Borno, dan Najeriyan da Turawa suka horar ya koma talla

Shekaru 35 yana aikin koyarwa a Borno, dan Najeriyan da Turawa suka horar ya koma talla

  • An samu wani dattijo da shafe shkaru 35 yana aikin karantarwa, amma daga karshe ya koma talla
  • An ce bayan ritayarsa ya koma aikin tallan man zafi saboda ya biya wa kansa bukatun yau da kullum
  • A cewarsa, shi Turawan Ingila ne suka ma karantar dashi, amma gashi yanzu yana tallan a kan titi

Borno - Bayan shekaru 35 yana hidimar aikin gwamnati a matsayin malamin makaranta a jihar Borno, wani dan Najeriya ya koma talla a kan titi don samun abin biyan bukata.

An ga Al-Amin Shettima Bello wanda ya yi ritaya daga aikin koyarwa yana tafe yana tallan man zafi da aka fi sani mantileta a Maiduguri, Daily Post ta ruwaito.

Hanyar da Bello ke bi wajen samun na abin ka ya kasance yana zama a kusa da cibiyar ATM ta Bankin First Bank a Monday Market ta Maiduguri don kwastomomi daga masu zuwa da banki ko ATM.

Bayan Shekaru 35 yana aikin koyarwa a Borno, dan Najeriya da Burtaniya ta horar ya koma talla
Malamin makarantan da ya koma talla | Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

An ga shaidar bayansa a wani faifan bidiyo da cibiyar sadarwa ta G-Role Africa ta yada a Facebook.

Me ya sa malamin da ya yi wa kasa hidima ya kare a talla?

Bello ya ce ya koma yin talla ne don samun abin biyan bukata ba saboda kada ya daura bukatunsa akan wani.

A cewar kwararren malamin, yawancin abokan karatunsa suna da abin hannu amma da yawa ba sa tuna akwai shi a duniya.

Turawan Ingila ne suka koyar da shi

Yayin da take tabbatar da cewa Turawan Ingila ne suka koyar da shi, Bello ya ce ya taba barin makaranta amma ya dawo karatu, godiya ga iyayensa, in ji rahoton Global Times.

Yace:

"Na yi aikin kafinta tsawon shekaru kafin iyayena suka yanke shawarar na sake komawa makaranta."

Abinda ka raina: Ana sayar da jakar 'Ghana-Must-Go' N860k a Amurka

A wani labarin, Hoton mashahuriyar jakar nan da matafiya ke saye don shake ta da kaya wato 'Ghana must go' ya bazu a yanar gizo inda jama'a ke martani kan yadda aka bayyana darajar kudi na jakar.

Lamarin ya girgiza jama'a da dama a kafar sada zumunta lokacin da aka ga an makalawa jakar farashi $2090 (N860,390.30) a wani shagon sayayya na yanar gizon mai Balenciaga na kasar Amurka.

Legit.ng ta leko wannan rubutun da wani mai suna @kennytrip2 ya wallafa a shafin sada zumunta tare da taken:

"Dakata .. meye? Shin ya kamata mu gaya musu?"

Asali: Legit.ng

Online view pixel