Ka yi wa sojojin da suka yi bore afuwa kamar yadda ka yi wa tubabban ƴan ta'adda, Falana ga Buhari

Ka yi wa sojojin da suka yi bore afuwa kamar yadda ka yi wa tubabban ƴan ta'adda, Falana ga Buhari

  • Femi Falana, babban lauya mai kare hakkin bil-adama ya bukaci Shugaba Buhari ya yi wa sojojin da aka samu da laifin bore afuwa
  • Sojojin dai an same su da laifin kin bin umurnin shugabanninsu ne a Maiduguri, jihar Borno inda suke yaki da yan ta'adda
  • Sojojin sun yi ikirarin cewa sun yi boren ne ga shugabanninsu saboda rashin isasun makamai da kayan aiki na ba su da shi
  • Falana ya ce idan har gwamnatin tarayya da na jihohi za su iya yi wa yan ta'adda afuwa ya kamata sojojin suma a yi musu afuwa

Legas - Babban lauyan Nigeria mai rajin kare hakkin bil adama, Femi Falana (SAN), ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa sojoji 70 da aka samu da laifin bore afuwa, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An kai hari NDA ne kawai don batawa gwamnatin Buhari suna, Mai magana da yawun shugaban kasa

An samu sojojin da laifin yi wa shugabanninsu bore a Maiduguri, Jihar Borno a shekarar 2014 kuma daga bisani aka yanke musu hukunci.

Ka yi wa sojojin da suka yi bore afuwa kamar yadda ka yi wa tubabban yan ta'adda, Falana ga Buhari
Sojojin Nigeria da aka samu da laifin yi wa shugabanninsu bore. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da farko an yanke wa sojojin hukuncin kisa amma a 2015, bayan Falana ya rika bibiyar shar'arsu, an sauya hukuncin zuwa daurin shekaru 10 a gidan gyaran hali.

A wata wasika mai dauke da kwanan wata na 25 ga watan Agustan 2021, da ya aike wa shugaban kasa, Falana ya ce sojojin kawai sun nemi a basu mukamai da suka dace ne domin yaki da yan ta'addan a arewa maso gabas.

A cewar rahoton na The Cable, Babban lauyan ya ce ba laifin sojojin bane cewa ba a samar musu da makamai da sauran abuwan da suke bukata ba.

Ya ce idan har gwamnati za ta karbar afuwar tubabbun yan ta'adda, sojojin da kawai nema suka yi a wadatar da su kayan aiki suma sun cancanci a yi musu afuwa.

Kara karanta wannan

Tattaunawa da Ortom: 'Yan jaridan Channels TV sun kwashe sa'o'i a hannun jami'an DSS

Mene wasikar Falana ta kunsa?

Wani sashi na wasikar ya ce:

"Kwamitin da shugaban kasa ya kafa kan binciken siyo makamai ya tabbatar da cewa wasu sojoji da farar hula sun karkatar da $2.1 biliyan da N643 biliyan. Sojojin da suka karkatar da kudaden ne suka yi wa yaki da ta'addancin zagon kasa."
"Duba da karkatar da kudaden makaman da sojojin da farar hular suka yi, kamata ya yi a tuhume su da bore, zagon kasa da laifukan yaki. Amma saboda rufa-rufa sai tsiraru daga cikinsu ne kawai hukumar EFCC ta tuhuma da karkatar da kudade.
"Har wa yau, Shugaban kasa ya yarda cewa an yi wa sojojin rashin adalci a hirar da BBC Hausa ta wallafa a ranar 28 ga watan Disamban 2015. A lokacin ya ce 'gwamnain wancan lokacin ta tura sojoji filin daga ba tare da makamai da kayan yaki ba. Wannan shine abin da yasa suke yi boren kuma aka kama su.

Kara karanta wannan

Kashe-Kashen Jos: CAN ta miƙa muhimman saƙo ga shugabannin musulmi da kirista a Plateau

"Kowa dai ya sani cewa gwamnatin tarayya da wasu gwamnatin jihohi sun yi wa yan ta'addan da suka dauki makami suka yaki Nigeria afuwa. Sojojin da aka yanke wa hukunci saboda sun nemi a basu makamai su yaki yan ta'adda ne suka fi cancantar afuwa daga gwamnatin tarayya."

Zulum Ya Ziyarci Faston Da Aka Kashe Ɗansa Yayin Rushe Coci a Borno Don Masa Ta'aziyya

A wani labarin daban, Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno ya ziyarci Bitrus Tamba, faston da aka kashe dansa yayin rushe cocin Ekklesiyar Yan’uwa Nigeria (EYN) da ke Maiduguri, babban birnin jihar, The Cable ta ruwaito.

Ezekiel Bitrus, dan faston na daga cikin wadanda suka yi zanga-zangar nuna kin amincewarsu da rushe cocin da hukumar BOGIS ta jihar Borno ta yi a watan Agusta.

A cewar rahoton na The Cable, jami'an tsaro da suka taho tare da BOGIS sun bude wa masu zanga-zangan wuta da nufin tarwatsa su amma harsashi ta samu Bitrus.

Kara karanta wannan

Hawaye sun kwaranya sakamakon kashe tsohon ɗan kwallon Nigeria da aka yi a rikicin Jos

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164