Nasara daga Allah: Sojoji sun kwace Rann, sa'o'i bayan farmakin mayakan ISWAP

Nasara daga Allah: Sojoji sun kwace Rann, sa'o'i bayan farmakin mayakan ISWAP

  • Zaman lafiya ya dawo Rann, jama'a sun koma harkokin su bayan sojoji sun yi nasarar fatattakar miyagun 'yan ISWAP
  • Kamar yadda masana wurin suka kimanta, a kalla daga Rann zuwa Maiduguri, babban birnin jihar Borno ya kai tazarar 350km
  • Majiyoyi masu karfi sun tabbatar da cewa mayakan ISWAP din sun isa wurin da yawan su suna harbe-harbe

Rann, Borno - Mayakan ISWAP sun kai wa sansanin soji da ke Rann farmaki, hedkwatar aiwatar da mulkin karamar hukumar Kala-Balge ta jihar Borno.

Tazarar Rann zuwa Maiduguri, babban birnin jihar Borno ya kai 350km.

Majiya masu karfi sun sanar da Daily Nigerian cewa mayakan ISWAP sun isa garin ne da yawansu inda suka yi ta harbe-harbe.

Nasara daga Allah: Sojoji sun kwace Rann, sa'o'i bayan farmakin mayakan ISWAP
Nasara daga Allah: Sojoji sun kwace Rann, sa'o'i bayan farmakin mayakan ISWAP. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Wasu mazauna yankin, musamman fararen hula sun yi ta tsere zuwa dazuka yayin da ma’aikatan jin kai suka yi ta tserewa wuraren Kamaru.

Kara karanta wannan

Mun yi sa'an samun Buhari matsayin Shugaban Kasa, Shehun Borno

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai labaran da suka riski Daily Nigerian sun tabbatar da cewa tun bayan farmakin komai ya dawo daidai a yankin.

Wasu mazauna yankin da aka tattauna dasu a safiyar Talata sun ce yawancin mazauna yankin sun koma gidajen su bayan sojojin kasa da na sama sun yi gaggawar kawo dauki.

An tattaro bayanai a kan yadda zaman lafiya ya dawo yankin tun bayan shugaban wata runduna, Christopher Musa ya bai wa rundunar soji umarnin gaggawar zuwa wurin don kwantar da tarzomar da kuma fatattakar ‘yan ta’addan.

An samu bayani a kan yadda rundunar wacce mai rikon kwaryar GOC na yanki na 7, Abdulwahab Eyitayo ya jagoranta suka yi ta ragargazar ‘yan ta’addan.

Wata musayar wuta ta auku tsakanin rundunar soji da wasu ‘yan ta’adda wacce ta kwashe sa’o’i ana yi. Daga nan ‘yan ta’addan suka samu suka sulale daga sansanin sojin.

Kara karanta wannan

'Yan ISWAP sun fatattaki mazauna daga gidajensu a jihar Borno zuwa kasar Kamaru

Sai dai sun ragargazu bayan sojojin sun bude musu wuta wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan ‘yan ta’addan da dama sannan wasun su suka tsere da miyagun raunuka,” kamar yadda wani jami’in binciken sirri ya sanar da The Nation.

Rikicin Jos: An tsananta tsaro a farfajiyar majalisar jihar Filato

A wani labari na daban, an tsananta tsaro a farfajiyar majalisar jihar Filato a safiyar ranar Litinin. Ponven Wuyep, magatakardan majalisar ya tabbatar da cewa an kara yawan jami'an tsaro amma kuma ana cigaba da aiwatar da sha'anonin mulki.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya musanta rade-radin da ke yawo na cewa an garkame majalisar jihar baki daya.

A'a, ba a rufe majalisar ba saboda ana cigaba da ayyuka kamar koyaushe. A halin yanzu ina cikin majalisar amma an kara jami'an tsaro kuma babu wanda ya ke cewa wani komai.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel