Mun yi sa'an samun Buhari matsayin Shugaban Kasa, Shehun Borno

Mun yi sa'an samun Buhari matsayin Shugaban Kasa, Shehun Borno

  • Mai Martaba Shehun Borno ya ce shugaba Buhari babban alherine ga al'ummarsa
  • Shugaban Majalisar dattawa ya kai ziyara jihar Borno
  • Sarkin ya bayyana farin cikinsa na mika wuyan yan ta'addan Boko Haram

Maiduguri, jihar Borno - Shehun Borno, Abubakar El-Kanemi, a ranar Litnin, ya ce mutan jihar Borno sun yi sa'an samun Shugaba Muhammadu Buhari matsayin shugaban kasa saboda gwamnatinsa ta rage ta'addanci.

Shehun ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, da ya kawo masa gaisuwan ta'aziyyar rashin 'yayansa, AriseTV ta ruwaito.

Ya ce al'ummarsa ta sha bakar wahala sakamakon rikicin Boko Haram amma sun yi sa'a gwamnatin shugaba Buhari na hanyan kawo karshen rikicin.

A cewarsa, dakarun Sojin Najeriya sun kwace dukkan kananan hukumomin dake karkashin Boko Haram a baya kuma mutane sun koma rayuwarsu kamar yadda suka saba a jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun fasa coci, sun yi awon gaba da masu ibada

Ya bayyana farin cikinsa kan yadda yan ta'addan Boko Haram ke mika wuya.

Mun yi sa'an samun Buhari matsayin Shugaban Kasa, Shehun Borno
Mun yi sa'an samun Buhari matsayin Shugaban Kasa, Shehun Borno
Asali: Depositphotos

'Yan ISWAP sun fatattaki mazauna daga gidajensu a jihar Borno zuwa kasar Kamaru

Kungiyar ISWAP ta kaddamar da wani gagarumin sabon hari a Rann, hedkwatar karamar hukumar Kala Balge a jihar Borno.

Bayanai sun ce mazauna garin da yawa sun tsere zuwa Kamaru sakamakon wannan harin.

Rann gari ne a jihar Borno dake da iyaka da kasar Kamaru.

Wani mazaunin garin ya ce maharan sun kyale fararen hula su bar garin ba tare da wani rauni ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel