Rikicin Jos: An tsananta tsaro a farfajiyar majalisar jihar Filato

Rikicin Jos: An tsananta tsaro a farfajiyar majalisar jihar Filato

  • Tsaro ya matukar tsananta a farfajiyar majalisar jihar Filato a safiyar Litinin, talatin ga watan Augusta
  • Magatakardan majalisar, Ponven Wuyep ya musanta labaran da ke yawo na cewa an rufe majalisar baki daya
  • A cewarsa, yanzu haka yana cikin majalisar kuma ana cigaba da ayyukan sha'anin mulki yayin da ma'aikata ke shige da fice

Jos, Filato - An tsananta tsaro a farfajiyar majalisar jihar Filato a safiyar ranar Litinin. Ponven Wuyep, magatakardan majalisar ya tabbatar da cewa an kara yawan jami'an tsaro amma kuma ana cigaba da aiwatar da sha'anonin mulki.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya musanta rade-radin da ke yawo na cewa an garkame majalisar jihar baki daya.

A'a, ba a rufe majalisar ba saboda ana cigaba da ayyuka kamar koyaushe. A halin yanzu ina cikin majalisar amma an kara jami'an tsaro kuma babu wanda ya ke cewa wani komai.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Gwamnan APC na fuskantar barazanar tsigewa kan rikicin makiyaya

Rikicin Jos: An tsananta tsaro a farfajiyar majalisa jihar Filato
Rikicin Jos: An tsananta tsaro a farfajiyar majalisa jihar Filato. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC
Asalin jami'an tsaron mu ne a kofar shiga. ma'aikata suna ta shige da fice kuma babu wata matsala, ya sanar da Daily Trust.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ranar Asabar, a yayin taron manema labarai, majalisar ta bukaci jama'ar jihar da su bai wa kan su kariya bayan rikicin da ke aukuwa a jihar a cikin kwanakin nan.

A wani harin tsakar dare da aka kai Yelwan Zangam a ranar Talata da ta gabata, an rasa rayukan mutum 37.

Wannan mummunan lamarin ya auku ne bayan mako daya da miyagu suka tare fasinjoji 27 suka sheke su yayin da suke kan hanya inda suka ratsa ta Jos.

A huɗubar Juma'a, Sheikh Nuru Khalid ya caccaki Buhari, yace ya bar ƴan bindiga suna mulki

A wani labari na daban, babban limamin masallacin Apo Legistlative Quarters, Sheikh Nuru Khalid, ya caccaki Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan kasa kawo karshen ta’addanci a kasar nan.

Kara karanta wannan

Kashe-kashe: Ku kare kanku, majalisar Filato ta bukaci mazauna jihar

Yayin hudubarsa ta ranar Juma’a, Limamin ya ce Buhari ya samu Najeriya a dunkule amma ya bar ‘yan ta’adda suna mulkar wani bangare na kasar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kuje ku fada wa shugaban kasa cewa a karkashin mulkinsa ne wasu bangare na jama’a suka fara bukatar mutane ba su kudade ko kuma su fuskanci farmaki,” a cewar Khalid.

Asali: Legit.ng

Tags:
Jos
Online view pixel