NDA: Babban malamin adddini ya aika gagarumin gargadi ga 'yan Najeriya, ya ce karin matsaloli na tafe

NDA: Babban malamin adddini ya aika gagarumin gargadi ga 'yan Najeriya, ya ce karin matsaloli na tafe

  • An gargadi 'yan Najeriya da su yi tsammanin karin matsaloli yayin da rashin tsaro da kasar ke ci gaba da yin kamari
  • Wannan gargadin ya fito ne daga bakin babban malamin addini, Rev. Father Ejike Mbaka, daraktan cocin adoration ministry, Enugu
  • Da yake ci gaba, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta saki Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB da aka haramta

Enugu, Nigeria - Daraktan cocin Adoration Ministry Enugu Nigeria, AMEN, Rev. Father Ejike Mbaka, ya aika da sakon gargadi ga ‘yan Najeriya.

Malamin ya fito fili ya bayyana cewa harin da aka kai a Kwalejin horon sojoji na Najeriya somin tabi ne na abin da zai riski Najeriya, jaridar Punch ta rahoto.

NDA: Father Mbaka ya aika gagarumin gargadi ga 'yan Najeriya, ya ce karin matsaloli na tafe
Father Mbaka ya aika gagarumin gargadi ga 'yan Najeriya kan halin da kasar za ta shiga Hoto: Nigeria presidency.
Asali: Facebook

Don haka ya bukaci gwamnatin Muhammad Buhari da ta canza tare da yin kira ga Allah da ya shiga cikin harkokin kasar, idan ana son kawar da matsalar.

Kara karanta wannan

Da dumi: Kotu ta soke dakatarwar da aka yi min a matsayin Shugaban APC, Oshiomhole ya bayyana mataki na gaba

Da yake ci gaba, Mbaka a cikin ta’aziyya yayin babban taro na ranar Lahadi ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta saki shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) Mazi Nnamdi Kanu, daga tsare.

Ya ce:

“Kamar yadda na gaya muku watanni biyu da suka gabata cewa abin da kuke gani shine somin tabi na matsala kuma babban matsalar tana zuwa. Wannan da suka yi (harin NDA) shine farkonsa. Bangare na biyu yana nan tafe.

“Kawai ina rokon Allah da ya shigo lamarin domin abin da ke faruwa a Afghanistan yanzu; idan Allah bai shirya ya taimake mu ba, halin da Najeriya ke ciki zai munana a nan gaba. Kuna da 'yanci ku kai wa Father Mbaka hari kuma ku soke ni, wannan shine matsalar ku."

Kara karanta wannan

Kashe-kashe: Ku kare kanku, majalisar Filato ta bukaci mazauna jihar

A wani labari na daban, mun kawo cewa 'Yan bindiga sun sace matan aure uku da wani mazaunin unguwar Zango a karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna.

Garin Zango yana makwabtaka da Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya, jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ‘yan bindigan sun isa yankin ne da tsakar daren Alhamis, suna ta harbe -harbe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel