Kashe-kashe: Ku kare kanku, majalisar Filato ta bukaci mazauna jihar

Kashe-kashe: Ku kare kanku, majalisar Filato ta bukaci mazauna jihar

  • An bukaci mazauna jihar Filato da su kare kansu daga hare-hare yayin da rikici ke ci gaba da kamari
  • Majalisar dokokin jihar Filato ce ta yi kiran inda ta yi ikirarin cewa tsaro na yau da kullun ba zai iya taimaka wa jama'a ba
  • A halin yanzu, 'yan majalisar sun aike da kudiri ga gwamna Lalong kan yadda za a maido da zaman lafiya a jihar

Filato - Majalisar dokokin jihar Filato ta nemi mazauna yankin da su kare kansu. Jihar ta fada cikin rikici a 'yan makonni biyu da suka gabata.

Da yake yiwa manema labarai jawabi a Jos, babban birnin jihar Filato, a ranar Juma’a, shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, Hon. Dasun Philip Peter, ya ce tsarin tsaro na yau da kullun ba zai iya ba da tabbacin tsaro ba.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Dalibin kwaleji ya yI barazanar sace 'Provost', ya shiga hannun hukuma

Kashe-kashe: Ku kare kanku, majalisar Filato ta bukaci mazauna jihar
'Yan majalisar dokokin Filato sun bukaci al'umman jihar da su kare kansu Hoto: Punch
Asali: UGC

Ya kuma ba Gwamna Simon Lalong makonni biyu ya yi aiki da kudurorin da ta gabatar masa kan yadda za a maido da zaman lafiya.

Peter ya ce 'yan majalisar za su dauki mataki idan gwamnati ta kasa daukar mataki cikin wa'adin makonni biyu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bukaci jami'an tsaro da su zakulo wadanda suka aikata wannan ta'asar tare da hukunta su kamar yadda doka ta tanada.

Ya ce:

“A madadin Majalisar Dokokin Jihar Filato, ina so in jajantawa Gwamnati da Jama’ar Jihar Filato kan kashe -kashen dabbanci da kisan gilla da ke faruwa a cikin garuruwan Bassa, Barkin Ladi, Bokkos, Jos ta Arewa, Jos ta Kudu , Mangu, Riyom, Jami’ar Jos da kuma na kwanan nan a Yelwa Zangam.
“Majalisar ta yi Allah wadai da dukkan wadannan kashe-kashen baki daya, duk wadannan kashe-kashen ba abin karba ba ne kuma abin Allah wadai ne. Muna jajantawa iyalan duk waɗanda suka rasa masoyansu a lokacin waɗannan hare-haren.

Kara karanta wannan

Ku Nemi Taimakon Ubangiji Kan Al'amuran Siyasarmu, IBB Ga 'Yan Najeriya

"Muna kira da babbar murya ga mutanen Filato da su tashi tsaye don kare kansu da garuruwansu, saboda tsarin tsaro na yau da kullun baya ba da tabbacin tsaron lafiyar mu a matsayin mu na mutane.”

Gwamnatin Zamfara ta ba da umarnin rufe kasuwanni da tashoshin man fetur, ta bayyana dalili

A wani labari na daban, an rufe dukkan manyan kasuwannin jihar Zamfara sakamakon umarnin Gwamna Bello Matawalle.

Kamar yadda gidan talabijin na Channels TV ya ruwaito, gwamnan ya kuma bayar da umurnin rufe dukkan gidajen mai dake yankunan.

Ya kuma ba da umarnin cewa kada a sayar da mai ko da a cikin jarkoki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng