‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu matan aure a Zariya

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu matan aure a Zariya

  • Wasu mahara da ake zaton 'yan bindiga ne sun kai hari yankin Zango da ke yankin Samaru a Karamar Hukumar Sabon Gari, Jihar Kaduna
  • A cikin haka suka yi garkuwa da wasu matan aure uku tare da wani namiji daya
  • An tattaro cewa 'yan bindigan sun isa yankin ne da tsakar daren Alhamis, suna ta harbe -harbe

'Yan bindiga sun sace matan aure uku da wani mazaunin unguwar Zango a karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna.

Garin Zango yana makwabtaka da Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya, jihar Kaduna.

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu matan aure a Zariya
Mahara sun yi garkuwa da wasu matan aure a Zariya Hoto: The Nation
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ‘yan bindigan sun isa yankin ne da tsakar daren Alhamis, suna ta harbe -harbe.

Lamarin na zuwa ne 'yan kwanaki bayan da ‘yan bindiga suka afkawa makarantar horar da sojoji ta Najeriya (NDA), inda suka kashe jami’ai biyu tare da yin garkuwa da wani babban soja.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An harbe mutum 11 har lahira a sabon harin da aka kai Katsina

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Jalige Mohammed, ya tabbatar da harin amma ya ce har yanzu rundunar ba ta samu cikakken bayanai ba kan lamarin, Aminiya ta ruwaito.

An harbe mutum 11 har lahira a sabon harin da aka kai Katsina

A wani labarin, mun ji cewa ‘yan bindiga sun harbe akalla mazauna kauyen Dan-Kumeji da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina 11 har lahira.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa mutane shida da suka samu raunuka a harin suna karbar magani a asibiti a yanzu haka.

Wani mazaunin garin, Abdulmumini Sani, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira ta wayar tarho, ya ce maharan sun afka wa kauyen da misalin karfe 11:30 na dare inda suka fara harbi ba kakkautawa.

Kara karanta wannan

Bayan shafe kwanaki 88, 'yan bindiga sun sako daliban Islamiyyar Tegina da suka sace

Asali: Legit.ng

Online view pixel