Da dumi: Kotu ta soke dakatarwar da aka yi min a matsayin Shugaban APC, Oshiomhole ya bayyana mataki na gaba

Da dumi: Kotu ta soke dakatarwar da aka yi min a matsayin Shugaban APC, Oshiomhole ya bayyana mataki na gaba

  • An soke umurnin kotu wanda ya dakatar da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam'iyyar APC
  • Oshiomhole ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Lahadi, 29 ga watan Agusta, game da matsayinsa a cikin jam’iyya mai mulki
  • Tsohon gwamnan na Edo ya kara da cewa duk da cewa an cire shi daga mukaminsa, ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da kasancewa memba na jam'iyyar APC

Abuja - Tsohon shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa Adams Oshimhole, yayi magana game da zama memba na jam'iyya mai mulki da kuma wasu hujjoji game da dakatar dashi daga ofis.

Oshiomhole ya ce kotun daukaka kara ta soke dakatarwar da aka yi masa a matsayin shugaban APC, makwanni biyu bayan da aka ba da umarnin farko, PM News.

Kara karanta wannan

Buhari ya yiwa 'yan bindiga masu AK-47 abun da ya fi ayyana su a matsayin 'yan ta'adda muni, Garba Shehu

Da dumi: Kotu ta soke dakatarwar da aka yi min a matsayin Shugaban APC, Oshiomhole ya bayyana mataki na gaba
Oshiomhole ya ce shawarar da APC ta yanke ba ta dame shi ba Hoto: APC
Asali: Facebook

Kalamansa:

"An yanke hukuncin kotun ne a ranar 2 ga watan Yuli, 2020, kusan makonni biyu bayan an cire ni daga ofis. Na yanke shawarar bayyana shi ne saboda na ga masu sharhi da yawa suna ba da shawarar cewa mutane ba su san cewa an yi watsi da karar ba."

Tsohon gwamnan na Edo wanda ya ce har yanzu shi dan APC ne mai himma ya lura cewa ya amince da batun cikin kyakkyawar zuciya ba tare da la'akari da doka ko haramcin dakatar da shi ba.

Ya ce:

“Na ce to, ba tare da la’akari da halacci ko haramcin batun ba, na yarda da abin da ya faru da zuciya daya kuma na dage kan yin duk abin da zan iya don tallafa wa jam’iyyar.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta ba da umarnin rufe kasuwanni da tashoshin man fetur, ta bayyana dalili

Shahararren dan siyasar ya bayyana cewa zai ci gaba da kasancewa mai kwazo da tasiri a cikin APC tare da fatan samun nasarar jam'iyyar a babban zaben 2023.

Tsohon Shugaban Jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole, Ya Fadi Abinda Ka Iya Faruwa da Yan Najeriya a 2023

A gefe guda, tsohon shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Adams Oshiomhole, ranar Asabar, yace yana fatan Allah ba zai bar yan Najeriya cikin matsala ba yayin da zaɓen 2023 ke kara gabatowa.

Oshiomhole ya faɗi haka ne a wurin bikin rantsar da Victoria Unoarumi a matsayin shugabar Rotary Club Abuja.

Yace ba wai ya shiga APC don ya zama shugabanta bane, sai don a kafa wata jam'iyya mai karfi da zata yi waje da PDP daga madafun iko, kamar yadda punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng