Dalilin da ya sa na ki daukar nauyin ginin CAN da kudaden gwamnati duk da cewa ni Kirista ne, Obasanjo

Dalilin da ya sa na ki daukar nauyin ginin CAN da kudaden gwamnati duk da cewa ni Kirista ne, Obasanjo

  • Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ya ki zuba kudaden gwamnati a CAN duk da cewa shi Kirista ne
  • A cewar tsohon Shugaban kasar, Prelate Sunday Mbang ne ya nemi ya gina Cibiyar Kiristocin ta Kasa
  • Obasanjo ya ce ya ki karbar shawarar ne domin idan ya yi hakan, tilas ne ya yi wa Musulmai da sauran mabiya addinai suma

Cif Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban Najeriya, ya bayyana dalilin da ya sa ya ki daukar nauyin ginin kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) da kudin gwamnati a lokacin da yake kan mulki.

Tsohon Shugaban kasar, mai shekara 85, ya ce idan ya yi wa Kiristoci, ba shi da wani zabi illa ya yi makamancin haka ga mutanen sauran addinai a kasar, Punch ta ruwaito.

Dalilin da ya sa na ki daukar nauyin ginin CAN da kudaden gwamnati duk da cewa ni Kirista ne, Obasanjo
Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya ce ya ki amfani da kudin gwamnati wajen gina kungiyar CAN Hoto: Laolu Thomas
Asali: Getty Images

Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 27 ga watan Agusta, a jihar Legas yayin wani taron kaddamar da littafin da murnar zagayowar ranar haihuwar Eminence Prelate na 85.

"Idan na yi wa Kiristoci, dole ne in yi wa sauran mutane"

Obasanjo, wanda ya yi mulki a matsayin zababben shugaban kasa ta hanyar dimokuradiyya tsakanin watan Mayun 1999 zuwa watan Mayun 2007, ya ce Mbang, wanda yanzu masanin ilimin likitanci ne, ya bukace shi da ya “kawo kudi don kammala Cibiyar Ecumenical.”

OBJ ya ce, duk da haka, ya ki duk da cewa shi Kirista ne domin idan ya yi hakan, dole ne ya ci gaba da raba albarkatun tsakanin sauran mabiya addinai daban -daban a kasar, jaridar The Punch ta ruwaito.

"Shi (Mbang) ya tambaye ni a matsayinsa na shugaban kungiyar Kiristoci a Najeriya cewa ya kamata in kawo kudi don kammala Cibiyar Ecumenical kamar yadda suke kiranta a lokacin, yanzu an san ta da Cibiyar Kiristoci ta Kasa.

"Na ce, 'A'a, ba zan yi ba; ba zan sanya kudin gwamnati a cikin irin wannan ba domin idan na yi wa Kiristoci, dole ne in yi wa Musulmi, dole ne in yi wa Babalawo (mabiya addinin gargajiya), Dole ne in yi wa masu bautar Sango. A'a. "

Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya samu gagarumin mukami a waje

A wani labarin, kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta nada tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo a matsayin babban wakili a yankin gabashin Afirka.

Shugaban hukumar AU, Moussa Mahamat ne ya sanar da nadin na Obasanjo a ranar Alhamis, 26 ga watan Agusta, jaridar The Cable ta ruwaito.

A cewar Mahamat, babban aikin Obasanjo shine samar da zaman lafiya, tsaro, da kwanciyar hankali na siyasa ta hanyar tattaunawa a yankin wanda ya hada kasashe kamar Djibouti, Eritrea, Ethiopia, Somalia, Kenya, Sudan, Sudan ta Kudu, da Uganda, jaridar The Guardian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel