Da dumi-dumi: Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya samu gagarumin mukami a waje

Da dumi-dumi: Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya samu gagarumin mukami a waje

  • Yanzu Cif Olusegun Obasanjo ne babban wakilin Kungiyar Tarayyar Afirka a yankin gabashin Afirka
  • Tsohon shugaban zai inganta zaman lafiya da tsaro a yankin na Afirka wanda ya kunshi kasashe kamar Habasha, Somalia, Kenya, Sudan, Sudan ta Kudu, da Uganda
  • A cewar kungiyar, an zabi Obasanjo ne saboda kaunarsa ga nahiyar da kuma gogewarsa a fagen siyasar Afirka

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta nada tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo a matsayin babban wakili a yankin gabashin Afirka.

Shugaban hukumar AU, Moussa Mahamat ne ya sanar da nadin na Obasanjo a ranar Alhamis, 26 ga watan Agusta, jaridar The Cable ta ruwaito.

Da dumi-dumi: Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya samu gagarumin mukami a waje
An nada tsohon shugaban kasar a ranar Alhamis, 26 ga watan Agusta Hoto: Olusegun Obasanjo
Asali: Facebook

A cewar Mahamat, babban aikin Obasanjo shine samar da zaman lafiya, tsaro, da kwanciyar hankali na siyasa ta hanyar tattaunawa a yankin wanda ya hada kasashe kamar Djibouti, Eritrea, Ethiopia, Somalia, Kenya, Sudan, Sudan ta Kudu, da Uganda, jaridar The Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Gwamnonin PDP sun kira taron gaggawa domin su dinke baraka

Wani bangare na bayanin nadin ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Wannan shawarar na cikin shirin kungiyar Tarayyar Afirka na inganta zaman lafiya, tsaro, kwanciyar hankali da tattaunawar siyasa a duk fadin yankin na yankin gabashin Afirka.
"Musamman, babban wakilin zai kara himma tare da duk masu ruwa da tsaki na siyasa da masu ruwa da tsaki a yankin don samar da dawwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin yankin na gabashin Afirka."

Shugaban ya bayyana cewa an zaɓi dattijon ne don rike wannan mukamin saboda gogewarsa ta siyasa, da azamarsa ga manyan manufofi da haɗin kan yanki gami da zurfin ilimin na halin da yankin ke ciki a yanzu.

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana dalilan aikata laifuka a Najeriya.

A cewarsa, ta’addanci, fashi da makami na karuwa a Najeriya sakamakon karuwar yawan mutanen kasar. A zahirin gaskiya, tsohon shugaban kasar ya ce wannan yana hana shi barci cikin dare.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Boko Haram sun shiga tasku, sojojin Najeriya sun hada kai da na Rasha

Asali: Legit.ng

Online view pixel